Labarai Morganable Hausa

Shirin Kafa Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammala

Shirin Kafa Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammala. Yunkurin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba.

Najeriya Na Dab Da Kafa ’Yan Sandan Jihohi
Yan Sandan
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Yunkurin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan da za su tabbatar da amincewa da dokar.

A farkon wannan mako, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisun dokokin jihohi 30 sun amince da ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi.

A ranar Alhamis, shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya tabbatar da cewa ana sa ran kammala shirin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi kafin ko a cikin watan Disamban 2026.

Da yake tsokaci kan ƙudirin, Bamidele ya ce amincewar da kusan majalisun dokokin jihohi 30 suka bayar ta cika sharaɗin samun goyon bayan aƙalla kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar, kamar yadda Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, ya tanada.

A ƙarƙashin wannan tanadi, ana buƙatar amincewar majalisun dokokin jihohi aƙalla 24 daga cikin jihohi 36 na ƙasar kafin a ci gaba da aiwatar da matakan kafa rundunonin ’yan sandan jihohi.

Sanata Ali Ndume, ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Dattawa, ya shaida wa BBC cewa abin da ya rage yanzu shi ne Majalisar Dokokin Tarayya ta yanke mataki na gaba.

Ya ce: “Za a gabatar da batun a gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda za mu sake yin muhawara kafin mu kaɗa ƙuri’a kan amincewa da matakin ko kuma ƙin amincewa da shi.”

Sanatan ya ƙara da cewa domin ƙudirin ya samu karɓuwa, ana buƙatar goyon bayan kashi biyu bisa uku na mambobin majalisun dokokin tarayya.

A cewarsa, bayan kammala wannan mataki, za a miƙa ƙudirin ga shugaban ƙasa domin ya sanya hannu, wanda hakan zai ba da damar mayar da shi doka tare da fara shirye-shiryen aiwatar da shi.

Babban lauya kuma masani kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Barista Sanusi Musa, SAN, ya bayyana cewa matakin da ya rage bayan amincewar da ake buƙata shi ne miƙa ƙudirin ga shugaban ƙasa domin ya sanya hannu.

Ya ce: “Da zarar an miƙa ƙudirin ga shugaban ƙasa, yana da kwanaki 30 domin ya amince da shi ta hanyar sanya hannu, ko kuma ya yi gyare-gyare ya mayar da shi majalisa domin ta sake duba sauye-sauyen da ya gabatar.”

A cewar babban lauyan, idan shugaban ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin, zai zama doka, sannan a fara shirye-shiryen aiwatar da tanade-tanadensa.

Barista Sanusi Musa ya ce abin da amincewa da dokar ke nufi shi ne Najeriya za ta ba jihohi damar kafa rundunonin ’yan sanda nasu.

Sai dai ya bayyana cewa hakan ba yana nufin dole ne kowace jiha ta kafa rundunar ’yan sandanta ba.

Ya ce: “Abin da hakan ke nufi shi ne an bai wa jihohi damar kafa ’yan sandan jihohi. Don haka, duk jihar da take son kafa nata rundunar za ta gabatar da ƙudiri a majalisar dokokinta domin samun amincewa.”

Ya ƙara da cewa da zarar majalisar dokokin wata jiha ta amince da ƙudirin, jihar za ta iya kafa rundunarta domin ta fara aiki.

Amma idan wata jiha ba ta da buƙatar kafa irin wannan runduna, ba dole ba ne ta yi hakan.

Wata tambaya da ta dade tana jan hankalin ’yan Najeriya ita ce yadda za a rarraba ayyuka da ikon rundunar ’yan sandan jihohi da kuma rundunar ’yan sandan tarayya.

Barista Sanusi ya ce Kundin Tsarin Mulki ne zai fayyace yadda kowace runduna za ta gudanar da ayyukanta.

Ya bayyana cewa da zarar shugaban ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin, Majalisar Dokoki za ta tsara iyakokin iko da nauyin da ke kan kowace runduna.

A cewarsa, idan aka samu karo ko saɓani tsakanin ayyukan rundunonin biyu, Kundin Tsarin Mulki zai tanadi yadda za a warware matsalar, tare da bai wa rundunar ’yan sandan tarayya fifiko a irin waɗannan yanayi.

A yayin muhawarar da aka yi kan ƙudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Majalisar Dattawa ranar Laraba, shugaban masu rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele, ya ce idan ƙudirin ya zama doka, Najeriya za ta kasance da rundunonin ’yan sanda iri biyu.

Waɗannan su ne Rundunar ’Yan Sandan Tarayya da kuma rundunonin ’Yan Sandan Jihohi.

Sai dai kafin kowace jiha ta kafa rundunarta, dole ne ta fara samar da dokar da za ta kafa ta, sannan dokar ta bi ƙa’idojin da Majalisar Tarayya ta shimfiɗa.

Sai dai ƙudirin ya kuma tanadi yanayin da rundunar ’yan sandan tarayya za ta iya shiga cikin harkokin tsaron jiha a wasu lokuta na musamman.

Hakan na iya faruwa idan aka samu matsalar rashin bin doka da oda mai tsanani a wata jiha, ko kuma idan gwamnan jihar ya nemi taimakon gwamnatin tarayya. 

Ƙudirin ya tanadi cewa gwamnonin jihohi za su samu ikon zaɓar waɗanda za su zama kwamishinonin ’yan sandan jihohinsu daga cikin jami’an rundunar da ke aiki a jihar, tare da ba su ikon bayar da umarni kai tsaye kan harkokin tsaro.

Sai dai naɗin ba zai kammala ba har sai majalisar dokokin jihar da kuma hukumar kula da ayyukan ’yan sanda sun amince da shi.

Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu, ya ce wannan tsari ya yi kama da yadda ake naɗa manyan alƙalan jihohi. A irin wannan tsari, gwamna na iya gabatar da sunan wanda yake so, amma hukumar da aka ɗora wa alhakin tantancewa ce ke da ikon amincewa da naɗin.

Adaramodu ya ce: “Idan gwamna ya zaɓi kwamishinan ’yan sanda, za a miƙa sunansa ga hukumar kula da ayyukan ’yan sanda ta tarayya, wadda za ta binciki tarihinsa da cancantarsa kafin ta amince da naɗin.”

Ƙudirin ya kuma ƙunshi wasu tanade-tanade da aka tsara domin hana amfani da rundunonin ’yan sandan jihohi ta hanyoyin da ba su dace ba.

Ɗaya daga cikin tanade-tanaden shi ne cewa kwamishinan ’yan sandan jiha ba zai zama tilas ya bi umarnin gwamna da ya saɓa wa doka ba. A maimakon haka, yana da damar kai rahoton irin wannan umarni ga hukumar kula da ’yan sanda ta ƙasa.

An haramta amfani da rundunar ’yan sandan jiha wajen biyan buƙatun siyasa, ƙabilanci, addini, yanki ko kuma muradun wani mutum na kansa.

Majalisar Tarayya kuwa za ta ci gaba da tsara ƙa’idojin ɗaukar jami’ai aiki, horas da su, tantance cancantarsu, ƙarin girma da kuma ladabtar da jami’an ’yan sanda.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights