Mazauna Birnin Tudu Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama da 30
Mazauna Birnin Tudu Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama da 30. Al’ummar ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara.

Mahangar Labari
KANO —
Al’ummar ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara sun bayyana cewa sun kashe wasu ’yan bindiga sama da 30 bayan artabu da su kayi dasu na tsawon kwanaki uku.
Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa mazauna yankin sun ɗauki matakin tunkarar ’yan bindigar ne sakamakon hare-haren da suke fuskanta, lamarin da ya sa suka gaji da ci gaba da kasancewa cikin barazana da tsoro.
Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa BBC cewa sun fara shirin kare kansu ne bayan sun samu labarin cewa ’yan bindigar na shirin kai musu hari.
Ya ce “Da suka zo, muka buɗe musu wuta, su ma suka riƙa harbe-harbe, mu kuma muna mayar da martani. Sun tafi da wasu daga cikin mutanenmu, amma mu ma mun kashe da dama daga cikinsu.
“Mun ga wasu daga cikinsu waɗanda ba ƴan Najeriya ba ne.” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayan artabun, sun gano gawarwakin mutum 18 ko 19 a wurin da aka fafata, yayin da ’yan bindigar suka kwashe wasu daga cikin gawarwakin nasu.
A cewarsa, ’yan bindigar sun kasance kowane babur akwai mutum uku a kai, sannan kuma sun bar gawarwakin waɗanda suka kasa ɗauka a wurin da aka yi artabun.
Gwamnatin Zamfara ta ɗauki matakan ƙarfafa tsaro
Jafaru Ƙaura, mai ba wa gwamnan jihar Zamfara shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin inganta tsaro, kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da kuma hana ’yan bindigar sake dawowa don kai wasu hare-hare.
Ƙaura ya kuma ce adadin ’yan bindigar da mazauna ƙauyen suka kashe yayin artabun ya haura 30.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Haka kuma, ya yi kira ga mazauna Birnin Tudu da sauran ƙauyukan da ke kusa da yankin da su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar sanar da su duk wani motsi na shakku ko alamar da za ta iya nuna barazanar tsaro.
Ya jaddada cewa haɗin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da al’umma na da muhimmanci wajen gano masu hannu a ayyukan ta’addanci da kuma dakile yiwuwar sake aukuwar hare-hare ko kuma rasa rayuka.
Captin Abdullahi Bakoji (mai ritaya) ya yaba wa mazauna Birnin Tudu bisa matakin da suka ɗauka na kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Ya bayyana cewa kare kai na daga cikin haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ’yan ƙasa.
A cewarsa ‘‘Bai kamata a ce ko yaushe ana zuwa a kama ka kamar kaza ba., a je a daure ka a daji ana cutar da kai sannan a karbi kudade ba, shi kansa tsohon daraktan DSS ya taɓa jan hankaln mutane a kan hakan’’
Sai dai ya gargaɗi mazauna yankin cewa bai kamata su yi sakaci da tsaro ba, domin akwai yiwuwar ’yan bindigar su sake haɗuwa su dawo domin ɗaukar fansa kan abin da ya faru.
Bakoji ya shawarci al’ummar da su ƙara shiga cikin shiri wajen gudanar da ayyukan tsaron sa-kai, tare da tsara yadda za a riƙa gadin ƙauyen dare da rana domin hana masu kai hare-hare samun damar kutsawa cikin garin.
“Su ƙara shiri, su daina barci. Idan wasu sun yi barci, a samu wasu da za su tsaya su yi gadin gari. Sannan a sanar da jami’an tsaro, su ma su bayar da gudummawarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shi.
Wani mazaunin Birnin Tudu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun far wa garin ne ba zato ba tsammani, a daidai lokacin da mazauna yankin suka sassauta matakan tsaro da suka saba bi.
Ya ce, “Abin da ya faru a Birnin Tudu cikin kwanaki ukun da suka gabata ya tayar musu da hankali. ’Yan bindigar sun kewaye garinmu ba zato ba tsammani. A kullum muna cikin shirin ko-ta-kwana da kare kanmu, amma a wannan karon mun yi zaton babu wata matsala.”
Ya ƙara da cewa, “Kafin mu ankara, sun riga sun kewaye garin ta kowane ɓangare. Sun zo su da mutum uku-uku a kan kowane babur. Akwai babura sama da 100. Ni da kaina na ƙirga guda 71 daga inda na ɓoye.”
A cewarsa, bayan isowar maharan, sun shiga garin suna harbe-harbe, tare da fasa shaguna da kwashe kayayyakin da ke ciki.
Ya bayyana cewa mazauna garin sun zaɓi tunkarar maharan domin kare kansu da gidajensu, maimakon su tsere su bar garin.
Ya ce, “Muna godiya ga Allah da wasu daga cikin mutanenmu suka kasance a shirye domin kare garin. Mun tunkare su ne saboda guduwa daga gidajenmu mu zama ’yan gudun hijira zai zama abin kunya a gare mu.”
Mazaunin garin ya ce mutane uku ne suka rasa rayukansu a yayin artabun, yayin da wasu uku suka samu karaya, wani mutum kuma ya samu raunin harbin bindiga.
Ya kuma bayyana cewa maharan sun sake kai hari karo na biyu a lokacin da mazauna garin ke rabon batir ɗin fitilu.
Ya ce, “Mun sake tunkarar su, daga ƙarshe kuma muka fatattake su zuwa yankin gabashin garin. Suna da yawa, kuma duk suna ɗauke da makamai.”
A ƙarshe, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tafi da shanun da suka sace daga wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da Birnin Tudu, amma ba su yi nasarar satar dabbobin da ke cikin garin ba.
Al’ummar gari da gwamnati sun yaba wa mutanen garin Tudu kan jarumtar da suka nuna wajen kare rayukansu, dabbobinsu, yayansu, matansu da kuma dukiyoyinsu.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







