Sabon Bashin Da Tinubu Ke Son Karbowa
Sabon Bashin Da Tinubu Ke Son Karbowa. Yan hamayya da Masana Tattalin Arziƙi sun soki bashin da Tinubu ke son kara karbowa.

Mahangar Labari
KANO —
’Yan Hamayya da Masana Tattalin Arziƙi Sun Soki Shirin Tinubu na Ɗaukar Sabon Bashi. ’Yan jam’iyyun hamayya da wasu masana tattalin arziƙi a Najeriya na ci gaba da nuna adawa da sabon shirin Shugaba Bola Tinubu na karɓar bashin kuɗi daga ƙasashen waje.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dokokin Najeriya, inda ya nemi amincewarta domin karɓar sabon bashin dala biliyan 20.51.
A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen magance ƙarancin ababen more rayuwa da kuma cike gibin kuɗaɗen da ake buƙata a muhimman sassan tattalin arziƙi da walwalar al’umma.
Tinubu ya ce fannonin da za a mayar da hankali a kansu sun haɗa da samar da wutar lantarki, sufuri, kiwon lafiya, ilimi, noma, samar da ruwa, tsaro, samar da ayyukan yi da kuma inganta tsarin tafiyar da harkokin kuɗi.
Ya bayyana cewa an zaɓi ayyukan ne bayan tantance su, domin tabbatar da cewa za su taimaka wajen rage talauci, bunƙasa ƙwarewa da sana’o’i, tare da ƙarfafa samar da isasshen abinci a ƙasar.
Shugaban ya kuma ce ya miƙa buƙatar ga Majalisar Dokoki domin a duba ta tare da amincewa da ita cikin gaggawa, ta yadda za a fara aiwatar da ayyukan da aka tsara.
Sai dai wannan mataki ya jawo suka daga ’yan hamayya, waɗanda ke zargin gwamnatin da rashin bayyana cikakkun bayanai kan yadda za a kashe kuɗaɗen bashin.
Jagoran hamayyar ƙasar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Majalisar Dokoki da kada ta amince da sabon bashin har sai gwamnati ta fito da cikakken bayani kan ayyukan da za a gudanar da kuɗaɗen da su.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce bai kamata majalisar ta amince da karɓar “ko dala ɗaya ba” matuƙar gwamnati ba ta bayyana cikakkun bayanai kan kowane aiki ko kwangila da za a aiwatar.
Ya ce ya kamata a bayyana kuɗin da za a ware wa kowane aiki, sunayen ’yan kwangilar, sharuɗɗan bashin da kuma tsarin da za a bi wajen biyan kuɗaɗen.
Sanarwar ta ƙara da cewa Atiku ya ce wannan sabon yunƙuri ya tabbatar da gargaɗin da ya yi a ranar 12 ga Oktoba, game da shirin gwamnati na neman bashin da ya kai kusan dala biliyan 20.
Ya kuma soki Shugaba Tinubu bisa rashin bayyana cikakkun bayanai kan yadda za a kashe kuɗaɗen, yana mai cewa ambaton manyan fannoni kamar ilimi, lafiya da sufuri kaɗai bai isa ya tabbatar da dacewar neman irin wannan bashin mai yawa ba.
Ita ma jam’iyyar NDC ta soki shirin karɓar sabon bashin, tana mai cewa matakin na iya ƙara tsananta matsalolin tattalin arziƙin Najeriya.
A wata hira da BBC, daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Ibrahim Hussaini Abdulkarim, ya zargi gwamnatin Tinubu da mayar da neman bashi wata babbar hanyar tafiyar da tattalin arziƙin ƙasar.
“Ƙasa ce ta rikici kullum, ba abin da ake ji sai neman bashi. Wannan al’amari ya sa ’yan ƙasar sun rikice,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu na mamakin yadda gwamnatin da ta bayyana cewa tana ɗaukar matakan farfaɗo da tattalin arziƙi ke ci gaba da neman ƙarin bashin kuɗi.
Abdulkarim ya ce gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur tare da ƙara haraji a wani yunƙuri na inganta tattalin arziƙin ƙasar, amma duk da haka tana ci gaba da neman rancen kuɗaɗe masu yawa.
“Gwamnatin ce fa ta cire tallafin man fetur, ta kuma ƙara kuɗin haraji, duk a yunƙurinta na inganta tattalin arziƙi, amma har yanzu ta ci gaba da karɓar manyan basuka,” in ji shi.
Dokta Murtala Abdullahi Kwara, malami a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’adua da ke Katsina, ya ce bai yi mamakin sabon buƙatar bashin da Shugaba Tinubu ya gabatar ba.
A cewarsa, tun a kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar a shekarar da ta gabata, an nuna cewa za a samar da wani kaso mai yawa na kuɗaɗen kasafin ne ta hanyar karɓar bashi.
Ya ce wasu ’yan Najeriya na da dalilin nuna shakku kan yadda gwamnati ke amfani da kuɗaɗen da take karɓa a matsayin bashi.
Dokta Kwara ya bayyana cewa rashin aiwatar da babban kaso na kasafin kuɗin da gwamnati ke gabatarwa a kowace shekara na iya ƙara haifar da tambayoyi kan yadda ake gudanar da harkokin kuɗaɗen jama’a.
“Gwamnatin da ta kwashe fiye da shekara uku a kan karagar mulki ba ta iya aiwatar da kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin da take yi kowace shekara ba, ai kowane ɗan ƙasa zai fahimci cewa su ke kiɗansu kuma su yi rawansu,” in ji shi.
Masanin tattalin arziƙin ya ce ya kamata waɗanda ke goyon bayan karɓar sabon bashin su riƙa tambayar gwamnati irin ayyukan da ta gudanar da kuɗaɗen da ta karɓa a baya, tare da neman sanin yadda za ta yi amfani da sabon bashin.
Dokta Murtala Abdullahi Kwara ya bayyana cewa ci gaba da karɓar basuka na iya haifar da matsaloli daban-daban ga tattalin arziƙin Najeriya.
Ya ce a baya-bayan nan, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi tsokaci kan nauyin kuɗin ruwa da Najeriya ke biya kan basussukanta, wanda a cewarsa ya zarce kuɗaɗen shigar da ƙasar ke samu.
“In ji shi, idan ƙasa ta shiga irin wannan yanayi, hakan na iya jefa tattalin arziƙinta cikin haɗari.”
Ya ƙara da cewa yawan dogaro da bashin ƙasashen waje na iya rage amincewar masu zuba jari da sauran ƙasashe ga tattalin arziƙin Najeriya.
A cewarsa, wannan yanayi na iya ƙara matsin lamba kan darajar naira, ya haifar da tashin farashin dala da kuma ƙara hauhawar farashin kayayyaki. Haka kuma, yana iya taimakawa wajen ƙara matsalolin rashin aikin yi.
Masanin ya kuma bayyana wasu matakan da yake ganin za su taimaka wajen rage dogaron Najeriya ga karɓar basuka.
Ya ce matakin farko shi ne magance matsalolin da ke addabar tattalin arziƙin ƙasar, tare da ɗaukar matakan da za su ƙarfafa samar da kuɗaɗen shiga.
Haka kuma, ya shawarci gwamnati da ta sake duba yadda take gudanar da harkokinta, tare da rage kuɗaɗen da take kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ƙara da cewa ya kamata a mai da hankali wajen magance hauhawar farashin kayayyaki da kuma samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya.
Ya jaddada muhimmancin inganta tattalin arziƙin ƙasar ta yadda za ta samu damar biyan buƙatunta ba tare da dogaro da karɓar manyan basuka a kai a kai ba.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







