Labarai Morganable Hausa

An Kara Kudin Shiga Gidajen Kallon Kwallo A kano

A Kara Kudin Shiga Gidajen Kallon Kwallo A kano. Ƙungiyar masu gidajen kallon wasannin ƙwallon ƙafa ta Jihar Kano ta kara kudi.

An Kara Kudin Shiga Wuraren Kallon Kwallo A kano
Hoton mutane a gidan kallon kafa
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Ƙungiyar masu gidajen kallon wasannin ƙwallon ƙafa ta Jihar Kano ta sanar da ƙarin kuɗin kallon wasanni daga naira 200 zuwa naira 500.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon hauhawar kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan kuɗin tashoshin talabijin, lasisi, haraji da wutar lantarki.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugabancin ƙungiyar ya fitar, inda ya ce sabon tsarin zai fara aiki daga ranar Talata, 3 ga Nuwamba, saboda tsadar gudanar da gidajen kallon wasanni.

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta sake jaddada cewa ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan kuɗin tashoshi, lasisi, haraji da wutar lantarki ne suka tilasta mata ƙara kuɗin shiga.

Sai dai binciken da jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa wasu gidajen kallon ƙwallo da ke unguwanni daban-daban a cikin birnin Kano sun ƙara kuɗin shiga da naira 100 kacal, inda kuɗin ya tashi daga naira 100 zuwa naira 200.

A Ƙaramar Hukumar Bichi kuwa, shugaban ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallo, Murtala Maijangwam Bichi, ya bayyana cewa kuɗin shiga zai ƙaru daga naira 100 zuwa naira 200.

Ya kuma buƙaci al’ummar yankin da su fahimci sabon tsarin, bisa la’akari da ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da gidajen kallon.

A wani ɓangare kuma, matsalar kuɗi da ke addabar wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a gasar Firimiyar Najeriya ta zama ruwan dare. A wasu lokuta, ƙungiyoyin kan kasa zuwa wasannin da za su buga a wajen garuruwansu saboda rashin kuɗin sufuri, abinci, masauki da sauran kuɗaɗen gudanar da tafiya.

Irin wannan matsala ta dade tana addabar gasar Firimiyar Najeriya, amma har yanzu gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa ba su fara ɗaukar ingantattun matakan magance ta ba, duk da cewa akwai hanyoyin da za a bi wajen kawo ƙarshenta.

A ranar Litinin, 1 ga wannan wata, rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta kasa zuwa Jihar Abia domin buga wasan gasar Firimiyar Najeriya da za ta fafata da takwararta ta Enyimba International, da ke garin Aba, sakamakon rashin kuɗi.

Lamarin ya tayar da hankalin magoya bayan ƙungiyar da sauran masu sha’awar ƙwallon ƙafa a ƙasar, kasancewar hakan ya sake bayyana irin matsalolin da ke fuskantar ci gaban ƙwallon ƙafa a Najeriya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar da aka fi sani da “Sai Masu Gida” ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta yi jigilar ’yan wasanta da masu horar da su zuwa Jihar Abia.

Wata majiya ta tabbatar wa jaridar Leadership Hausa cewa rashin isassun kuɗaɗe ne ya hana ƙungiyar tafiya buga wasan. Majiyar ta ƙara da cewa a lokuta da dama ƙungiyar kan nemi aron kuɗi domin gudanar da tafiye-tafiyen wasanninta na waje, amma a wannan karon ta kasa samun wanda zai ba ta bashin.

Sai dai daga baya, an samu sanarwar cewa gwamnatin Jihar Kano ta samu labarin halin da ƙungiyar ke ciki, inda ta bayar da umarnin a yi jigilar ’yan wasan zuwa Jihar Abia ta jirgin sama.

Haka kuwa aka yi, inda ’yan wasan suka isa jihar ta Abia ta jirgin sama, kuma ba a dage wasan ba, domin an fafata a lokacin da aka tsara tun farko. Rashin isa wurin wasan a kan lokaci ne ya sa aka nemi a dage shi.

Sai dai matsalar ƙarancin kuɗi da ke addabar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya ba sabon abu ba ne. A wannan kakar ma, an dage wasan Kano Pillars da Abia Warriors sakamakon matsalar kuɗi da ƙungiyar Abia ta fuskanta.

An taɓa dage wasan Gombe United da Remo Stars saboda rashin kuɗi a hannun ƙungiyar Gombe United.

Tun da farko dai, Kano Pillars ta rubuta wa hukumar da ke kula da gasar Firimiyar Najeriya wasiƙa, inda ta sanar da cewa ba za ta iya isa wurin wasan a kan lokacin da aka tsara ba, tare da neman a mayar da wasan zuwa ranar Alhamis, maimakon ranar Laraba 3 ga wannan wata.

Sai dai daga ƙarshe, ƙungiyar ta samu damar tafiya garin Aba ta jirgin sama, kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa da jaridar Leadership Hausa.

Ana ganin cewa wannan mataki ba shi ne mafita ta dindindin ba, domin babu tabbacin cewa gwamnati za ta iya ci gaba da jigilar ’yan wasa ta jirgin sama a duk lokacin da za su buga wasa a wata jiha.

Akwai wasu jihohin da ba su da filayen saukar jiragen sama, wanda hakan ke nufin cewa dole ne a sauka a wata jiha da ke maƙwabtaka da su, sannan a ci gaba da tafiya ta mota zuwa inda za a buga wasan.

Lamarin ya jawo martani daga masu bibiyar harkar ƙwallon ƙafa a Najeriya, inda da dama suka nuna rashin jin daɗinsu tare da bayyana cewa abin da ya faru abin kunya ne.

Sun bayyana cewa ƙungiya mai girman tarihi da matsayi kamar Kano Pillars bai kamata ta dogara kacokan da gwamnati wajen samun kuɗaɗen gudanar da harkokinta na yau da kullum ba, idan har ana son ta samu ci gaba mai ɗorewa.

Masu sukar lamarin na ganin cewa ya kamata shugabannin gudanarwar ƙungiyar su fahimci cewa abin kunya ne su jagoranci ƙungiya kamar Kano Pillars, amma a riƙa jiran sai gwamnati ta ba ta kuɗin gudanarwa kafin ta iya gudanar da ayyukanta.

A cewarsu, hakan na nuna gazawar shugabannin wajen zamanantar da ƙungiyar da kuma samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da za su taimaka mata wajen tafiyar da harkokinta.

Sun kuma bayyana cewa ya kamata ƙungiyar ta samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga har ta kai matsayin da za ta iya tallafa wa gwamnati da kuɗi, kamar yadda manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya ke yi.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights