Labarai Morganable Hausa

Wane Ci Gaba Aka Samu A Bangaren Wutar Lantarki?

Wane Ci Gaba Aka Samu A Bangaren Wutar Lantarki?. Jam’iyyar APC ta kare alƙawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kafin zaɓen 2023.

Wane Ci Gaba Aka Samu A Bangaren Wutar Lantarki?
Hoton Abin Wutan Lantarki
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Jam’iyyar APC ta kare alƙawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kafin zaɓen 2023 na kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a Najeriya cikin shekaru huɗu na farkon mulkinsa.

Martanin jam’iyyar ya biyo bayan sukar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC ya yi wa Tinubu, bisa zargin gaza cika alƙawarin da ya ɗauka na magance matsalar wutar lantarki.

Matsalar wutar lantarki na daya daga cikin manyan ƙalubalen da suka daɗe suna addabar ’yan Najeriya. A lokuta daban-daban, shugabanni da ’yan siyasa kan yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar yayin yaƙin neman zaɓe.

Jam’iyyar ADC mai hamayya ta soki Shugaba Tinubu bisa abin da ta bayyana a matsayin gazawarsa wajen cika alƙawarin da ya yi wa ’yan Najeriya kan samar da wutar lantarki a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar, ya ce Tinubu ya shaida wa ’yan Najeriya cewa kada su sake zaɓensa a karo na biyu idan ya gaza samar da wutar lantarki.

Sanarwar ta bayyana Tinubu yana cewa: “Kada ku zaɓe ni a karo na biyu idan na gaza samar da wutar lantarki.”

Ologbondiyan ya bayyana cewa wannan babban alƙawari ne da Tinubu ya ɗauka a lokacin da yake neman amincewar al’ummar ƙasar domin ya zama shugaban ƙasa. Ya ce saboda haka ’yan Najeriya na da haƙƙin tantance ayyukan gwamnatinsa bisa wannan alƙawari.

ADC ta ƙara da cewa babu wani yunƙurin sauya ma’anar kalaman shugaban ƙasar ta hanyar zaɓen wasu sassan jawabinsa, ƙara wasu bayanai ko amfani da dabarun nahawu da zai iya sa ’yan Najeriya su manta da alƙawarin da ya yi.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa maimakon gwamnatin Tinubu ta inganta samar da wutar lantarki tare da rage wa masu amfani da ita nauyi, ta mayar da hankali ne kan ƙara kuɗin wutar lantarki, yayin da ake ci gaba da samun katsewar wuta da amfani da tsarin ƙiyasta kuɗin wutar da masu amfani da ita suke sha.

A nata martanin, jam’iyyar APC ta ce Shugaba Tinubu ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya cika alƙawarin da ya ɗauka na inganta ɓangaren wutar lantarki.

A cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu, Dele Alake, ya fitar, ya ce ya kamata a yi la’akari da cikakken alƙawarin da shugaban ƙasar ya yi a shekarar 2023, maimakon mayar da hankali kan ɓangaren da ya yi magana kan samar da wutar lantarki kawai.

Alake ya ce ADC ta yi watsi da wani ɓangare na kalaman Tinubu, inda ya ce shugaban ƙasar ya kuma yi alƙawarin yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani idan ya gaza cimma manufar da ya sanya a gaba.

Ya bayyana cewa matsalar wutar lantarki a Najeriya ta daɗe fiye da shekaru 50, saboda haka ba abu ne da za a iya magancewa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba.

APC ta jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi watsi da alƙawarin da ta ɗauka ba, kuma tana ci gaba da ƙoƙarin kawo sauyi a ɓangaren wutar lantarki.

Jam’iyyar ta ce an samu wasu ci gaba a fannin samar da wutar lantarki tun bayan hawansa mulki.

Daga cikin matakan da APC ta ambata akwai sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023, wadda ta bai wa gwamnatocin jihohi damar shiga harkokin samarwa da rarraba wutar lantarki.

Ta bayyana cewa wasu jihohi sun fara cin gajiyar wannan doka ta hanyar kafa hukumomin kula da harkokin wutar lantarki da kuma jawo hankalin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu.

Alake ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan biyan tarin basussukan da suka dabaibaye kamfanonin samar da wutar lantarki da na iskar gas.

Gwamnatoci daban-daban kan bayyana cewa sun samu ci gaba a fannin samar da wutar lantarki a lokacin mulkinsu.

A wani hira da BBC tayi da Dr Abdurrahman Umar Lawan, ƙwararren masani kan makamashin lantarki a Najeriya, kuma malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, domin jin ko an samu wani ci gaba a fannin tun bayan hawan gwamnatin Tinubu.

Masanin ya bayyana cewa ana auna ci gaban da aka samu a ɓangaren wutar lantarki ne ta fuskar abubuwa huɗu, waɗanda suka haɗa da sauye-sauyen da aka kawo, yadda ake aiwatar da su, yawan wutar da ake samarwa da kuma wadda ake rarrabawa.

Ya ce ta fuskar sauye-sauye, an samu ci gaba, domin a cewarsa gwamnati ta bullo da wasu tsare-tsare masu inganci waɗanda aiwatar da su zai taimaka wajen inganta ɓangaren.

Ya ƙara da cewa akwai wasu tsare-tsaren da aka fara tun lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, waɗanda suka taimaka wajen inganta harkokin wutar lantarki a Najeriya.

“Ta wannan fuska akwai tsare-tsare da gwamnatin Najeriya ta yi tun lokacin mulkin Buhari, waɗanda suka taimaka wajen inganta harkokin lantarkin,” in ji masanin.

Ya ce sakamakon waɗannan sauye-sauye, jihohi 17 sun riga sun kafa dokokin da suka shafi samar da wutar lantarki a jihohinsu.

Sai dai Dr Abdurrahman ya bayyana cewa ba a samu irin wannan ci gaba ba ta fuskar aiwatar da tsare-tsaren.

Dangane da yawan faɗuwar babban layin wutar lantarki na ƙasa kuwa, masanin ya ce an samu ci gaba a shekarar 2026 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ƙididdigar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta nuna cewa an samu ƙaruwar yawan wutar lantarkin da ƙasar ke samarwa tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026, wato lokacin da Tinubu ke mulki.

A cewar bayanan hukumar, yawan wutar lantarkin da ake samarwa ya ƙaru daga GWh 34,942 a shekarar 2022 zuwa GWh 39,209 a shekarar 2026.

Game da faɗuwar babban layin wutar lantarki kuwa, NERC ta bayyana cewa ya faɗi sau shida a shekarar 2022, yayin da a shekarar 2024 ya faɗi sau tara.

Sai dai a shekarar 2025, babban layin wutar lantarkin ya faɗi sau biyu kacal.

Sai dai bayanan hukumar sun nuna cewa babban layin wutar lantarkin ya faɗi sau biyu a farkon shekarar 2026.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights