Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Hukuncin Kisa
Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Hukuncin Kisa. Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa mutane biyu, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mahangar Labari
KANO —
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa mutane biyu, Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kisan kai.
Gwamnatin Jihar Kano ce ta gurfanar da mutanen bisa zargin haɗa baki wajen aikata kisan kai da kuma ɓoye laifin.
Waɗanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ƙoƙarinsu na ƙwace takardun mallakar filin mamacin.
Da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Fatima Adamu ta Kotun mai lamba 18 da ke Miller Road, ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara, ƙarƙashin jagorancin Lauya Salisu Muhammad Tahir, sun gabatar da isassun hujjoji da suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar mutanen da su.
Kotun ta samu Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da laifin kashe Alhaji Dahiru, mazaunin Yankusa, ta hanyar caka masa wuƙa.
Kotun ta same su da laifin haɗa baki da Sadik Sanusi, wanda ake zargin ya yi amfani da babur mai kafa uku na haya wajen kai su wurin da suka aikata kisan, kafin daga bisani suka ƙona gawar mamacin.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa waɗanda ake tuhumar sun aikata kisan ne da nufin ƙwace takardun mallakar filin mamacin.
Kotun ta samu Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da laifin kashe Alhaji Dahiru, mazaunin Yankusa, ta hanyar soka masa wuƙa.
A wani hukuncin kuma, BBC ta rawaito cewa wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifuka daban-daban.
Kotun ta same su da laifin cinna wuta da kuma amfani da makami, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar.
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayyana cewa ta yi la’akari da bayanai da shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatar kafin ta zartar wa mutum na farko hukuncin kisa.
Mutum na farko, mai shekara 22, ya samu hukuncin ne bayan kotun ta same shi da laifin cinna wa wasu ’yan gida uku wuta a gidansu da ke unguwar Gayawa, cikin Ƙaramar Hukumar Gaya ta jihar.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Barista Lamido Soron Ɗinki, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a watan Satumban 2019.
Ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya shiga gidan ne ɗauke da jarkar mai, sannan ya zuba man a jikin ɗakunan da mutanen gidan suke kwance, kafin daga bisani ya cinna wa gidan wuta.
A cewarsa, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutanen da ke gidan, waɗanda suka haɗa da maigidan, Aminu, matarsa da kuma ’yarsu guda ɗaya.
Barista Soron Ɗinki ya ƙara da cewa bayan masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu, wanda ake zargin shi ma ya yi bayani a gaban kotu. Daga bisani kotun ta yanke masa hukuncin kisa bayan ta tabbatar da cewa shi ne ya aikata kisan.
Mutum na biyu kuma, kotun ta same shi da laifin caccaka wa kishiyar mahaifiyarsa wani abu, tare da shaƙe ƙanwarsa har ta mutu a unguwar Rijiyar Zaki, cikin Ƙaramar Hukumar Ungogo.
Barista Soron Ɗinki ya bayyana cewa an aikata laifin ne a watan Janairun 2023.
Ya ce: “Wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo gida ya nemi abinci, amma bai samu ba. Tun da farko ma, ya daɗe yana zargin kishiyar mahaifiyarsa da hana shi abinci, lamarin da ya fusata shi har ya ɗauki doguwar sukundireba ya caccaka mata a wuya.”
Ya ƙara da cewa bayan caka wa kishiyar mahaifiyarsa sukundireba, wanda ake zargin ya kuma farmaki wata yarinya da ke gidan, inda ya yi amfani da ɗankwali ya shake ta har ta mutu.
Sai dai lauyan wanda aka samu da laifin kashe kishiyar mahaifiyarsa, Mubarak Abubakar, ya bayyana cewa ba su gamsu da hukuncin ba, kuma za su ɗaukaka ƙara.
Ya ce: “Muna ganin cewa shaidun da aka gabatar guda biyu ne, wato mahaifinsa da kuma ɗan sandan da ya gudanar da bincike kan lamarin. Muna da damar yin tambayoyi kan wasu bayanan da suka bayar. Mun shaida wa kotu cewa waɗannan bayanai ba su wadatar wajen gamsar da kotu har ta same shi da laifi ba.”
Lauyan ya ƙara da cewa al’umma na da damar neman a duba takardun da suka shafi shari’ar domin su tabbatar da yadda aka gudanar da komai bisa tanadin doka.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin lauyan wanda ake tuhuma da cinna wa miji da matarsa wuta, amma ba ta samu nasara ba.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa na da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90, kamar yadda doka ta tanada.
A wani bangaren kuma Babbar kotun jihar Kano ta bada umarnin tsare wasu mutane uku kan zargin garkuwa da kuma kashe wani yaro mai suna Aliyu Haidar a ƙauyen Gobirawa da ke Ƙaramar Hukumar Rano ta jihar.
Lamarin ya faru ne bayan an hada baki da mai yin aikatau a gidan su Aliyu, inda ta fito dashi daga gida sannan ta mika sa izuwa hannun abokanan aikinta.
An gurfanar da su a gaban kotun bayan an zarge su da garkuwa da Aliyu, neman kudin fansa da kuma hadin baki wanda daga karshe da basu samu biyan bukata ba suka kashe Aliyu.
Sede bayan an karanta musu tuhumar da ake musu da karanto musu laifukan su, sun musanta aikata laifukan. Lauyoyin masu gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Soran Dinki tare da Barista Iliyasu Ibrahim, ne suka gabatar da waɗanda ake zargin a gaban kotun.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







