NCDC Ta Ɗauki Matakai Kan Matafiya Akan Ebola
NCDC Ta Ɗauki Matakai Kan Matafiya Akan Ebola. A dauki kwakwaran Matakai kan matafiya akan cutar Ebola da ta shigo.

Mahangar Labari
KANO —
Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta faɗaɗa shirin tantance matafiyan da ke shigowa ƙasar daga ƙasashen waje, ta hanyar buƙatar su cike fom ɗin bayyana halin lafiyarsu, bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja, Babban Birnin Tarayya.
Daraktan-janar na hukumar, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi.
A cewarsa, da farko NCDC ta wajabta cike fom ɗin ga dukkan matafiya da ke shigowa Najeriya daga ƙasashen waje. Sai dai daga baya hukumar ta takaita matakin ga matafiyan da suka fito daga ƙasashen da ake dangantawa da ɓarkewar cutar Ebola, ciki har da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da Uganda.
“Amma bayan bullar cutar, mun sauya wannan mataki,” in ji shi.
Idris ya bayyana cewa hukumar ta aika da sanarwar gargaɗi ga Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) da kuma Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA). Ya ce a halin yanzu suna jiran ƙarin umarnin da za su tsara yadda za a aiwatar da matakan tare da haɗin gwiwar kamfanonin jiragen sama.
Daraktan-janar ɗin ya ce shirin Najeriya na shirin ko-ta-kwana kan cutar an fi mayar da hankali ne kan manyan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa guda biyar da ke Legas, Abuja, Enugu, Kano da Fatakwal.
Ya ce jami’an kula da lafiyar matafiya a mashigai, wato Port Health Services, sun yi haɗin gwiwa da ma’aikatan filayen jiragen sama, jami’an shige da fice da kuma na kwastam domin ƙarfafa matakan shiri da tantance lafiyar mutanen da ke shigowa ƙasar.
A cewar Idris, NCDC na buƙatar haɗin kan hukumomin da ke kula da harkokin jiragen sama, saboda ba ita ce ke da ikon gudanar da ayyukan filayen jiragen sama kai tsaye ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa nau’in cutar Ebola da aka gano a Abuja shi ne Bundibugyo, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da ɗaukar matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar. Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu babu takamaiman magani ko allurar rigakafi da aka amince da su domin yaƙi da wannan nau’in cutar.
Bayanai sun nuna cewa majinyaciyar da aka gano tana ɗauke da cutar ta shigo Nijeriya daga ƙasar Uganda a ranar 3 ga Oktoba, ta jirgin saman Ethiopian Airlines. Wannan lamari ya jawo hankalin hukumomin lafiya, inda aka fara gudanar da bincike domin gano mutanen da suka yi hulɗa da ita da kuma waɗanda za su iya kasancewa cikin haɗarin kamuwa da cutar.
A wani mataki na ƙarfafa kariya daga cututtuka masu yaɗuwa, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun buƙaci a riƙa gudanar da binciken lafiyar dukkanin matafiya a filayen jiragen sama da tashoshin sufuri. Wannan mataki na nufin taimakawa wajen gano mutanen da suke ɗauke da cututtuka tun da wuri, domin hakan ze bada nasara wajen iya ɗaukar matakan da suka dace kafin matsalar ta ƙara karuwa.
Ya ce hukumomin da abin ya shafa suna aiki tare domin tabbatar da aiwatar da matakan da suka dace, yayin da jami’an shige da fice da na kwastam ke taka muhimmiyar rawa wajen sa ido a iyakokin Najeriya.
Idris ya kuma amince cewa ana fuskantar wasu ƙalubalen gudanar da aiki a filin jirgin saman Legas sakamakon ayyukan gine-ginen da ake yi a wurin.
Ya bayyana cewa NCDC za ta tattauna da FAAN da NCAA domin nemo hanyoyin magance matsalolin da ke kawo cikas ga ayyukan jami’an kula da lafiyar matafiya.
Ya ƙara da cewa shiga wuraren filayen jiragen saman da aka keɓe saboda dalilan tsaro na buƙatar bin ƙa’idojin tsaron da aka shimfiɗa.
Ƙarfafa tantance matafiya na daya daga cikin matakan da Najeriya ta ɗauka bayan tabbatar da bullar cutar Ebola mai nau’in Bundibugyo a Abuja a ranar 20 ga Oktoba.
A cewar rahoton PREMIUM TIMES, matar da ta kamu da cutar ’yar ƙasar Uganda ce mai shekaru 42, wadda ta shigo Najeriya daga ƙasarta a ranar 3 ga Oktoba.
Ta fara nuna alamun cutar ne a ranar 6 ga Oktoba, kafin ta je asibiti inda daga baya aka tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar.
A yayin taron manema labaran na ranar Lahadi, Idris ya ce jami’an lafiya sun gano mutum 53 da suka yi hulɗa da majinyaciyar.
Ya bayyana cewa mutum 44 daga cikinsu suna da alaƙa da cibiyar lafiya da aka yi wa matar magani. Sauran mutum tara kuwa sun haɗa da ’yan gidanta, wasu mutanen da suka yi hulɗa da ita a wata cibiyar lafiya, da kuma mambobin tawagar hukumar lafiya ta FCT da suka tattara samfurin gwajin cutar.
Ya ce ana ci gaba da gano dukkan mutanen da suka yi hulɗa da majinyaciyar tare da sanya ido kan lafiyarsu.
A cewarsa, jami’an lafiya za su ci gaba da sa ido kan waɗannan mutane na tsawon kwanaki 21, wanda shi ne lokacin da ake ɗauka a matsayin mafi tsawon lokacin da alamun cutar Ebola za su iya ɗauka kafin su bayyana.
Wannan mataki zai taimaka wajen gano duk wanda zai fara nuna alamun kamuwa da cutar a cikin wannan lokaci.
Idris ya yi kira ga ’yan Najeriya da aka gano sun yi hulɗa da majinyaciyar da su ba jami’an lafiya cikakken haɗin kai. Ya jaddada cewa kasancewa cikin jerin mutanen da suka yi hulɗa da mai cutar ba yana nufin mutum ya kamu da cutar ba ne.
NCDC na ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa matakan kariya da dakile yaɗuwar cututtuka a cibiyoyin lafiya, inganta ayyukan dakunan gwaje-gwaje da kuma wayar da kan jama’a domin yaƙi da jita-jita da yaɗa bayanan ƙarya.
Hukumar ta shawarci ’yan Najeriya da su riƙa samun bayanai daga ingantattun majiyoyin lafiya da aka amince da su, tare da ba da haɗin kai ga matakan da ake ɗauka domin dakile yaɗuwar cutar yayin da bincike ke ci gaba.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







