Labarai Morganable Hausa

An Tsare Mutane Uku Kan Zargin Kashe Yaro

An Tsare Mutane Uku Kan Zargin Kashe Yaro. Ana zargin wasu mutane kan sace Yaro, Neman kudin fansa da kuma kashe yaron.

An Tsare Mutum Uku Kan Zargin Kashe Yaro
Hoton Kotu
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Babbar kotun jihar Kano ta bada umarnin tsare wasu mutane uku kan zargin garkuwa da kuma kashe wani yaro mai suna Aliyu Haidar a ƙauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Rano ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne bayan an hada baki da mai yin aikatau a gidan su Aliyu, inda ta fito dashi daga gida sannan ta mika sa izuwa hannun abokanan aikinta.

An gurfanar da su a gaban kotun bayan an zarge su da garkuwa da Aliyu, neman kudin fansa da kuma hadin baki wanda daga karshe da basu samu biyan bukata ba suka kashe Aliyu.

Sede bayan an karanta musu tuhumar da ake musu da karanto musu laifukan su, sun musanta aikata laifukan. Lauyoyin masu gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Soran Dinki tare da Barista Iliyasu Ibrahim, ne suka gabatar da waɗanda ake zargin a gaban kotun.

Alƙalin kotun mai lamba 13 ya bayar da umarnin tsare su a gidan yari, sannan ya ɗaga sauraron shari’ar har zuwa ranar 4 ga Disamba, 2026, domin fara sauraron shaidun masu gabatar da ƙara. A wannan rana ne ake sa ran fara sauraron shaidun da masu gabatar da ƙara za su gabatar domin ƙarfafa zarge-zargen da suke yi kan mutanen.

Umarnin tsare waɗanda ake zargin wani mataki ne na ci gaba da shari’ar, yayin da kotun za ta ci gaba da nazarin tuhume-tuhumen da kuma hujjojin da aka kawo mata, da kuma Wanda  za a gabatar a gabanta. A irin wannan yanayi, ana buƙatar masu gabatar da ƙara su gabatar da hujjoji masu gamsarwa domin tabbatar da zarge-zargen da suke yi wa waɗanda ake tuhuma gaskiya ne.

Lamarin ya sake jawo hankali kan haɗarin garkuwa da yara da kuma yadda masu aikata irin waɗannan laifuka kan yi amfani da kusanci ko amincewar iyalai wajen samun damar cutar da su. Zargin da ake yi a wannan shari’a ya nuna muhimmancin kulawa da tsaron yara, sanin irin mutanen da suke mu’amala dasu, irin mutanen da za’a kawo gida da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da bincike mai zurfi a duk lokacin da aka samu rahoton ɓacewar yaro ko kuma yiwuwar an yi garkuwa da shi.

Daya daga cikin waɗanda ake zargi na aikatau a gidansu yaron hakan yasa ta samu damar  awon gaba da Aliyu Haidar, ta kai shi wurin abokan aika-aikar ta. 

Aminiya ta ruwaito cewa wayenda ake zargin su uku sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan biyu daga wurin iyalan yaron.

Sai dai masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa rashin biyan kuɗin fansar ne ya sanya waɗanda ake zargin suka kashe yaron.

Masana harkokin tsaro da na shari’a sun sha jaddada muhimmancin gudanar da cikakken bincike a kan laifukan garkuwa da mutane, musamman idan abin ya shafi yara. Hakan na taimakawa wajen gano yadda lamarin ya faru, gano duk mutanen da ake zargin suna da hannu, da kuma tattara hujjojin da za su taimaka wa kotu wajen yanke hukunci bisa doka.

Haka kuma, ana ganin cewa haɗin gwiwa tsakanin iyaye, al’umma da jami’an tsaro na da muhimmanci wajen kare yara daga haɗarin garkuwa da su. Iyaye da masu kula da yara na buƙatar lura da mutanen da ke mu’amala da su, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro idan aka samu wani abin da ya tayar da hankali.

A wannan shari’a ta Aliyu Haidar, babban abin da ake jira shi ne fara sauraron shaidun masu gabatar da ƙara, domin kotu ta tantance sahihancin zarge-zargen da ake yi wa mutanen uku. Dole ne a ba waɗanda ake tuhuma damar kare kansu, yayin da masu gabatar da ƙara za su kasance da alhakin gabatar da hujjojin da suka dace.

Alkalin ya daga shari’ar don gano masu laifin, saboda kar a zalinci wayenda basu da laifi. Hakan na nuna cewa shari’ar dole se an nutsu, an tara hujjoji masu karfi, wayenda aka hada baki dasu da kuma yadda aka kashe Haidar kafin a yanke hukunci.

Sace sacen yara ya fara yawa, saboda a kwanakin baya an samu nasarar ceto yara sama da 100 da aka yi garkuwa da su daga cikin garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, da kuma yankunan da ke kewaye da shi.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan waɗanda ake zargi da aikata laifin satar yaran mata ne, waɗanda suka fito daga wasu jihohin yankin Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu na ƙasar.

Bayanan da jaridar Aminiya ta samu sun nuna cewa har yanzu akwai yara ƙanana da dama da aka sace, waɗanda ba a san inda aka kai su ba. Wannan na nuna cewa duk da nasarorin da ake samu wajen ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen gano sauran waɗanda suka ɓace da kuma cafke waɗanda ake zargi da hannu a cikin lamarin.

Daga cikin yaran da aka samu nasarar cetowa akwai yara 27 da aka gano a hannun wata mata mai suna Mary Yakubu. An kama matar ne a tashar mota da ke garin Bali, a lokacin da ake zargin tana ƙoƙarin tafiya da yaran da ta sace zuwa Jihar Edo.

Bayan kama Mary Yakubu, jami’an tsaro sun gurfanar da ita a gaban kotu domin fuskantar tuhumar da ake yi mata. Sai dai, har zuwa lokacin da rahoton ya fito, ba a samu cikakken bayani kan matakin da shari’ar ta kai ko kuma hukuncin da kotu ta yanke a kanta ba.

Yawaitar rahotannin satar yara ƙanana da manya a Jihar Taraba ya sa Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da wannan matsala. Hukumar ta ɗauki matakan gudanar da ayyukan ceto da kuma ƙoƙarin gano mutanen da ake zargi da safarar yara a sassa daban-daban na jihar.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights