Kungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Sheikh Masusuka
Kungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin kashe Sheikh Masusuka. Kungiyar Ansaru ta fito tace ita ta kashe Sheikh Masusuka.

Mahangar Labari
KANO —
Ƙungiyar ’yan ta’adda ta Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, wadda aka fi sani da Ansaru, ta bayyana cewa ita ce ta kashe fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Katsina da aka kashe Sheikh Yahaya Masusuka, kamar yadda PREMIUM TIMES ta gano.
An harbe malamin tare da wani abokinsa mai suna Adamu Abubakar a wajen gidansa da ke Dutsin-Ma a garin Katsina, a yammacin ranar Litinin.
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa wasu mutane biyu ɗauke da makamai, waɗanda suke kan babur, sun buɗe wa malamin da abokinsa wuta da misalin ƙarfe 7:30 na dare, wanda yayi sanadiyar mutuwar su.
Bayan faruwar lamarin, an garzaya da waɗanda harin ya rutsa da su zuwa wani asibiti da ke kusa domin samun kulawar likitoci, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Rundunar ’yan sandan sun fara gudanar da bincike kan kisan Malamin, tare da tura jami’an tsaro na musamman domin gano waɗanda suka aikata laifin da kuma kamo su.
Sheikh Masusuka ya shahara wajen koyar da addinin Musulunci bisa koyarwar Alƙur’ani, tare da ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar mu’amala tsakanin ’yan Najeriya da masu bin addinai daban-daban. Haka kuma, malamin ya kasance mai yin Allah-wadai da masu tsattsauran ra’ayi da kuma yaɗa akidun da ke ƙarfafa tashin hankali.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ita ma ta yi Allah-wadai da kisan malamin, inda ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin sun fuskanci hukunci.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa Sheikh Masusuka ya sha fuskantar barazana da tsoratarwa a lokacin rayuwarsa.
A cikin wani bidiyo mai tsawon mintuna huɗu da PREMIUM TIMES ta samu a ranar Talata, ƙungiyar Ansaru ta bayyana cewa mayaƙanta ne suka kashe Sheikh Masusuka da misalin ƙarfe 8:30 na dare.
Ƙungiyar ta ambaci malamin akan goyon bayan zaman lafiya da yake yadawa tsakanin mabiya addinai daban-daban, tare da wasu dalilai, a matsayin hujjojin da suka kai masa hari.
A cikin bidiyon, Ansaru ta kira marigayin da kalmar “arnai”, wadda take amfani da ita wajen bayyana mutumin da take ɗauka a matsayin wanda ba Musulmi ba. Ƙungiyar ta kuma ce tana “farin cikin” sanar da kisan da aka yi waɗanda ta kira da“sojojin Allah”.
“Masusuka arnai ne, ba Musulmi ba ne. An ɗauke shi aiki ne domin ya kawo cikas ga Musulunci da kuma rikitar da Musulmi,” in ji ƙungiyar.
Ansaru ta ƙara da cewa wasu malaman addini sun gayyaci Sheikh Masusuka domin gudanar da mukabala, wato muhawara kan batutuwan addini, amma malamin ya ƙi amincewa da gayyatar, a cewar ƙungiyar.
Baya ga ikirarin kashe malamin, ƙungiyar ta kuma yi barazana ga wasu mutanen da ta kira kafirai, waɗanda take zargi da raina hadisai na Annabi Muhammadu (SAW).
“Ku tuba, ku daina, in ba haka ba, muna nan zuwa gare ku,” in ji ƙungiyar a cikin barazanar da ta yi.
Taiwo Adebayo, wani mai bincike kan rikice-rikice da tsarin gudanar da tsaro a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Afirka (ISS Africa), ya bayyana kisan Sheikh Masusuka a matsayin wani lamari mai matuƙar tayar da hankali.
A cewarsa, lamarin ya nuna cewa barazanar Ansaru ba ta tsaya ga mamaye wasu yankuna kawai ba. Ya ce ƙungiyar na iya kai hari kan mutanen da ba su amince da akidunta ba, ko da kuwa suna zaune a wuraren da ke nesa da sansanoninta.
Binciken PREMIUM TIMES ya nuna cewa Ansaru na gudanar da ayyukanta a wasu sassan yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya, wasu shekaru bayan ƙungiyar ta ƙaura daga yankin Arewa maso Yamma.
A baya, hukumomin Najeriya sun gudanar da samame da dama domin murƙushe ayyukan ƙungiyar. A cikin wasu ayyukan da aka gudanar kwanan nan, an kama wasu daga cikin shugabanninta da suka haɗa da Abu Bara’a da Mallam Mamuda.
Sai dai, duk da ikirarin da Ansaru ta yi na ɗaukar alhakin kisan Sheikh Masusuka, ƙungiyar ba ta bayyana sunayen mutanen da ta ce sun aiwatar da harin ba.
Adebayo ya bayyana cewa ba lallai ba ne ƙungiyar ta tura mayaƙanta kai tsaye daga sansanoninta da ke yankin iyakar Najeriya da Benin domin kashe malamin.
A maimakon haka, ya ce akwai yiwuwar ƙungiyar ta yi amfani da ’yan bindigar yankin wajen gudanar da aikin, ko dai ta hanyar ɗaukar su aiki domin kai harin, ko kuma ta amfani da su wajen tattara bayanan sirri da suka taimaka wajen gano inda malamin yake.
A cewarsa, irin wannan dabara ta taɓa bayyana a farkon rikicin Boko Haram, lokacin da ƙungiyar ke aika mutane zuwa garuruwa domin kashe malaman addini da ’yan siyasa, yayin da shugabanninta ke fakewa a dazuzzuka.
Wannan bayani ya nuna yiwuwar amfani da mutanen da suka san yankin wajen tattara bayanan sirri da kuma aiwatar da hare-hare, ba tare da shugabannin ƙungiyar sun fito fili ba.
Ba a bayyana takamaiman mutanen da suka kashe Sheikh Masusuka ba, kuma har yanzu ana buƙatar binciken hukumomin tsaro domin gano waɗanda suka kai harin da kuma tabbatar da cikakken yadda aka tsara kisan.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







