Me Ya Sa INEC Ta Ki Amincewa Da Aminu Abdulsalam
Me Ya Sa INEC Ta Ki Amincewa Da Aminu Abdulsalam. Ana ci gaba da muhawara kan rashin sanya sunan ɗan takarar Jam’iyyar NDC.

Mahangar Labari
KANO —
Ana ci gaba da muhawara kan rashin sanya sunan ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, cikin jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar INEC ta fitar bayan nazarin korafe-korafen da jam’iyyu suka gabatar.
Sai dai yayin da wasu ke ganin an cire ɗan takarar gaba ɗaya daga takarar, Kwankwasiyya na murnar cewa INEC ta amince da shigar jam’iyyar NDC cikin zaɓen.
Kwankwasiyya ta bayyana farin cikinta ne bayan da INEC ta saka sunan jam’iyyar cikin sabon jerin sunayen ‘yan takarar zaɓen 2027 da ta fitar a ranar Juma’a.
Duk da haka, hukumar ba ta sanya sunan ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdulsalam ba. A maimakon haka, ta bayyana cewa akwai batun umarnin kotu da ya shafi takararsa.
Wannan na zuwa ne bayan cece-ku-cen da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen farko, inda ba a ga sunan Farfesa Isa Ali Pantami na PDP a jihar Gombe da kuma Aminu Abdulsalam na NDC a Kano ba.
Rashin sunayen ’yan takarar biyu ya jawo martani daga magoya bayan jam’iyyunsu, abin da ya sa INEC ta sanar da cewa za ta sake duba korafe-korafen da aka gabatar mata.
A makonnin baya, wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa INEC ta kammala nazarin korafe-korafen. Sai dai rahotanni sun bambanta, inda wasu suka ce za a mayar da sunayen Pantami da Aminu Abdulsalam, yayin da wasu suka nuna cewa Pantami kaɗai za a mayar.
A sabon jerin da hukumar ta fitar, an dawo da sunan Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe. Amma a Kano, INEC ta saka sunan jam’iyyar NDC, tare da bayyana cewa akwai batun umarnin kotu da ya shafi takarar Aminu Abdulsalam.
Da yake magana da BBC, sakataren ƙungiyar Kwankwasiyya, kuma ɗan takarar kujerar majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni a jam’iyyar NDC a Kano, Dokta Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata, ya bayyana matakin INEC a matsayin babbar nasara ga jam’iyyar.
“Wannan babbar nasara ce a gare mu. Da farko ma babu sunan NDC a cikin jerin, sannan babu sunan ɗan takararmu na gwamna. Bayan mun gabatar da ƙorafi da hujjoji, INEC ta duba ta gano babu wani dalili da zai hana saka jam’iyyarmu.”
Ya ce daga cikin hujjojin da suka gabatar akwai rajistar Aminu Abdulsalam da aka yi kafin ranar 10 ga Yuni, tare da takardun shaida da suka gabatar, waɗanda ya ce hukumar ta karɓa.
A cewarsa, babbar nasarar da suka samu ita ce tabbatar da cewa jam’iyyar NDC za ta shiga zaɓen.
Ƙofar Mata ya kuma shaida wa BBC cewa daga wajen INEC ne suka samu bayanin cewa akwai umarnin kotu da ya hana saka sunan Kwamared Gwarzo cikin jerin ’yan takarar gwamna. Ya ce a baya jam’iyyar ba ta da masaniya kan wannan batu.
“Abin da ake cewa shi ne akwai umarnin kotu da ake jira, ba hukuncin ƙarshe ba ne. Wasu ne suka je suka buƙaci kotu ta hana INEC saka sunan ɗan takararmu. Mu ma ba mu san da ƙarar ba, domin a ɓoye aka shigar da ita,” in ji Kofar Mata.
Ya ƙara da cewa lauyoyin jam’iyyar za su garzaya kotu domin neman warware matsalar.
“Ina tabbatar maka cewa za a iya warware wannan umarnin idan aka saurari dukkan ɓangarori. Ranar Litinin lauyoyinmu za su je kotu domin dubawa tare da gabatar da hujjojin kare haƙƙinmu,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko suna zargin wata jam’iyya da hannu a rikicin, Dokta Yusuf ya ce ba su da wata hujja kai tsaye da za su jingina zargin ga wata jam’iyya. Sai dai ya bayyana cewa siyasa ba ta rasa dabaru da ƙulle-ƙulle.
“Ba ma zargi kai tsaye, amma siyasa ba ta rasa ƙulle-ƙulle. Wataƙila wasu ne suka haɗa baki. Amma APC ba ta so ta shiga zaɓe da kowa a Kano ba. Abin da ya sa na faɗa haka shi ne za ka ga suna murna da zarar an ce babu sunan ɗan takararmu.”
Sai dai Ƙofar Mata ya ce yanzu murnar da ake yi ta koma cikin gida, saboda an tabbatar da cewa NDC za ta shiga zaɓen.
Jigon na NDC ya kuma yi iƙirarin cewa Kwankwasiyya na da babban tasiri a Kano, yana mai cewa magoya bayan tafiyar za su mara wa jam’iyyar baya a zaɓen 2027.
“Mutanen Kano sun san tsarin Kwankwasiyya kuma suna binsa. Tunda Kwankwasiyya tana cikin NDC, muna da yaƙinin cewa mutane za su zaɓe ta ko da lokacin ba a kammala shari’ar ba.”
Wannan ƙarin bayani ya zo ne bayan wani bincike da aka gudanar a ranar Asabar, 31 ga Oktoban 2026, ya nuna cewa har yanzu ba a saka sunayen Aminu Abdulsalam Gwarzo da mataimakinsa, Rabiu Mustapha, cikin sabon jerin sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu ba.
A cikin jerin sunayen, INEC ta rubuta kalmar “umarnin kotu” a wuraren da ya kamata a saka sunayen ɗan takarar gwamnan Kano na NDC da mataimakinsa. Wannan mataki ya jawo tambayoyi kan dalilin da ya sa ba a ga sunan Gwarzo ba, duk da cewa a baya hukumar ta bayyana amincewa da takararsa.
Sai dai bayanin jami’in ya nuna cewa rashin sanya sunan ɗan takarar cikin jerin ba yana nufin an soke takararsa ko kuma an ƙi amincewa da ita ba.
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Kano na NDC, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya ce jam’iyyarsu na ƙara samun farin jini da yawan magoya baya.
Gwarzo ya bayyana cewa cire sunansa daga jerin ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara fitarwa ya ƙara wa jam’iyyar farin jini tare da jawo mata ƙarin magoya baya gabanin zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2027.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







