Labarai Morganable Hausa

Daga Kaya Masu Nauyi Na Inganta Lafiya 

Daga Kaya Masu Nauyi Na Inganta Lafiya. Duk wani nau’in motsa jiki na taimakawa wajen tsawaita rayuwa, amma daga cikin nau’o’in atisaye.

Daga Kaya Masu Nauyi Na Inganta Lafiya
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Duk wani nau’in motsa jiki na taimakawa wajen tsawaita rayuwa, amma daga cikin nau’o’in atisaye, ɗaga kaya masu nauyi ne ke taimaka wa mutum ya ci gaba da kasancewa cikin ƙoshin lafiya da kuzari yayin da yake tsufa. Ga yadda za ku iya shigar da irin wannan atisaye cikin ayyukanku na yau da kullum inji Gorzelitz.

Zaku iya fara atisayen ku da abinda za ku iya, wanda bai fi karfin ku ba. Kamar motsa jiki, daga kaya masu nauyin da basu fi karfin ku ba, cin kayan nau’ikan abinci masu kyau.

Wannan na ɗaya daga cikin matakan da na ɗauka domin haɗa atisayen ɗaga kaya masu nauyi cikin rayuwata ta yau da kullum.

Akwai dalili mai muhimmanci da ya sa nake yin hakan. Idan aka yi maganar lafiya da motsa jiki, yawancin abokaina da muke zaune a unguwa ɗaya sun fi mayar da hankali kan atisayen ƙarfafa zuciya da numfashi (cardio). Muna ƙirga matakan da muke ɗauka a kullum, muna bibiyar gudun da muke yi, sannan muna hawan keke a ƙarshen mako. Wasu daga cikinmu ma kan shiga gasar gudun rabin marasau (half marathon) ko kuma triathlon lokaci zuwa lokaci.

Ko da yake irin waɗannan atisaye na inganta lafiya da taimakawa wajen tsawaita rayuwa, masana sun yi imanin cewa haɗa atisayen ɗaga kaya masu nauyi cikin tsarin motsa jiki zai taimaka wa mutum ya rayu cikin ƙoshin lafiya da jin daɗi har zuwa lokacin tsufa.

Ta kuma ba da shawarar cewa mutane su riƙa yin atisayen ture nauyi da kafaɗu, inda ta ce: “Baya ba ta taɓa yin ƙarfi fiye da kima ba.”

A cewarta, ƙarfafa tsokokin bayan jiki na da matuƙar muhimmanci wajen taimakawa mutum ya riƙa zama da tsayuwa yadda ya kamata, rage haɗarin kamuwa da ciwon baya, da kuma ƙarfafa ƙashin bayan mutum.

Idan kun fara jin cewa atisayen ya yi muku sauƙi, za ku iya ƙara nauyin da kuke ɗagawa, yawan maimaita atisayen ko kuma adadin zagayen da kuke yi. Hakan ya faru ne saboda jiki na saba da ƙalubalen da ake fuskantar da shi yayin da yake ƙara ƙarfi a hankali.

Phillips ya ce: “Ba lallai ne ƙarin ya zama mai yawa ba. Ƙananan ƙarin da ake yi akai-akai cikin watanni ne ke haifar da babban sauyi.”

Alal misali, a farkon fara atisayen plank, mutum na iya kasa riƙe wannan matsayi na tsawon daƙiƙu 15. Amma yayin da jikinsa ke ƙara ƙarfi, zai iya tsawaita lokacin a hankali.

Phillips ya ƙara da cewa ya kamata atisayen ya kasance mai ɗan wahala, amma kada ya kai matakin da zai gagari mutum.

Ya ce: “Ba kwa son barin wurin motsa jiki kuna jin kamar kun gama ƙarewa gaba ɗaya. Ku riƙa tafiya a hankali.”

A cewarsa, yin atisaye akai-akai ya fi ƙoƙarin yin abubuwa da yawa lokaci guda. Idan mutum yana jin kasala ko rashin ƙwarin gwiwa, ya kamata ya tuna cewa kamar sauran nau’o’in motsa jiki, yin kaɗan ya fi rashin yin komai.

Bincike ya nuna cewa yin atisayen ƙarfafa tsokoki akai-akai na ƙara wa mutum damar rayuwa na tsawon lokaci. Haka kuma, yana rage haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya da daji da ciwon sukari, tare da rage yiwuwar mutuwa da wuri.

Wani babban bincike ya gano cewa yin atisayen ƙarfafa tsokoki na tsawon minti 30 zuwa 60 a mako na da alaƙa da raguwar haɗarin mutuwa daga dukkan dalilai da tsakanin kaso 10 zuwa 17 cikin 100.

Wani sabon babban bincike ya nuna cewa amfanin motsa jiki ga lafiya na ƙaruwa yayin da mutum ke ƙara yawan lokutan da yake yin atisaye. Binciken ya gano cewa yin atisaye na tsakanin minti 90 zuwa sa’o’i biyu a mako na rage haɗarin mutuwa da wuri da kaso 13 cikin 100.

Bincike ya kuma nuna cewa mutane na amfana da wannan atisaye a duk tsawon rayuwarsu. Gorzelitz ya gano cewa manya masu shekaru sama da 70 da ke yin atisayen ɗaga kaya masu nauyi akai-akai na da ƙarancin haɗarin mutuwa idan aka kwatanta da waɗanda ba sa yin irin wannan atisaye.

“Musamman yayin da muke ƙara tsufa, muna iya ganin ingantuwar ayyukan jiki da ƙarfi, tare da ƙaruwa a yawan tsokoki,” in ji Gorzelitz.

Phillips ya bayyana cewa gina ƙarin tsoka na samar wa mutum kariya yayin da yake tsufa.

“Lokacin da rashin lafiya ko rauni ko tiyata ko kuma tsufa suka zo, kuma galibi suna zuwa, kana son ka kasance da ƙarin kariya. Ina kallon motsa jiki a matsayin wani asusun ajiyar kuɗin ritaya da kake ginawa domin kanka a nan gaba,” in ji shi.

Akwai fa’idodi da dama da atisayen ke samarwa ga lafiyar ƙwaƙwalwa. Gorzelitz ya ce zuwa ɗakin motsa jiki na iya sa mutum ya samu natsuwa da kwanciyar hankali.

“Abu ne da ke rage damuwa sosai; zuwa ɗakin motsa jiki da yin atisaye na iya taimakawa wajen kawar da yawan tashin hankali da damuwa,” in ji shi.

A cewar Gorzelitz da Phillips, muhimmin abin da zai taimaka wa mutum ya samu nasara shi ne zaɓar irin atisayen da zai iya yi cikin sauƙi, wanda kuma zai dace da salon rayuwarsa ta yau da kullum.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights