An Fitar Da Matar Da Ta Kawo Ebola
An Dauke Matar Da Ta Kawo Cutar Ebola . An fitar da matar data kawo cutar Ebola daga Najeriya zuwa Switzerlan.

Mahangar Labari
KANO —
Matar mai shekaru 42 da ta kamu da nau’in kwayar cutar Ebola ta Bundibugyo, an ɗauke ta daga Najeriya a yau safiyar Litinin zuwa Switzerland domin ta cigaba da jinya a chan.
Hukumomin lafiya sun gano mutane 53 da suka yi mu’amala da majinyaciyar, inda aka killace su tare da ci gaba da sa ido kan lafiyarsu.
An ɗauki matar mai shekaru 42, wadda aka tabbatar da ta kamu da nau’in cutar a jirgin sama na musamman da misalin ƙarfe 6:00 a jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Ali Pate, ya tabbatar da cewa majinyaciyar ta bar Abuja zuwa Switzerland tare da mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun cutar ba.
Pate ya ce yanayin lafiyar majinyaciyar ya inganta sosai, tana cikin kwanciyar hankali, cikin hayyacinta kuma tana iya magana da mutane.
Ya ƙara da cewa sakamakon gwaje-gwajen jininta na dakin gwaje-gwaje ya kusa komawa yadda yake kafin ta kamu da cutar.
Ministan ya yaba wa ma’aikatan lafiyar da suka kula da mara lafiyar da kuma jami’an lafiyar da suka tsara kwashe ta bisa ƙa’idojin tsaron da aka tanada. Ya ƙara da cewa za a fitar da ƙarin bayani bayan majinyaciyar da mijinta sun isa inda za su je lafiya.
Sai dai ya yi gargadi cewa alamar saukin da take nunawa ba ya nufin ta warke gaba daya ba, saboda haka akwai bukatar ci gaba da kula da matakan kariya a kanta.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa nau’in cutar Ebola da aka gano a Abuja shi ne Bundibugyo, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da ɗaukar matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar. Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu babu takamaiman magani ko allurar rigakafi da aka amince da su domin yaƙi da wannan nau’in cutar.
Bayanai sun nuna cewa majinyaciyar da aka gano tana ɗauke da cutar ta shigo Nijeriya daga ƙasar Uganda a ranar 3 ga Oktoba, ta jirgin saman Ethiopian Airlines. Wannan lamari ya jawo hankalin hukumomin lafiya, inda aka fara gudanar da bincike domin gano mutanen da suka yi hulɗa da ita da kuma waɗanda za su iya kasancewa cikin haɗarin kamuwa da cutar.
A wani mataki na ƙarfafa kariya daga cututtuka masu yaɗuwa, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun buƙaci a riƙa gudanar da binciken lafiyar dukkanin matafiya a filayen jiragen sama da tashoshin sufuri. Wannan mataki na nufin taimakawa wajen gano mutanen da suke ɗauke da cututtuka tun da wuri, domin hakan ze bada nasara wajen iya ɗaukar matakan da suka dace kafin matsalar ta ƙara karuwa.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun bayyana cewa kiran ‘yan majalisar nada muhimmancin domin hakan ze sa a sanya ido kan lafiyar matafiya, musamman waɗanda ke shigowa ƙasar daga ƙasashen waje.
Binciken lafiya a wuraren shiga da fita na iya taimakawa wajen gano alamomin da ke buƙatar ƙarin kulawar likitoci, ko kuma gano mutanen da ya kamata a duba su domin kare sauran al’umma ko kuma shigo da wani sabon abu da ze iya cutar da mutane.
Bayan an dauke majinyaciyar da mijinta zuwa Switzerland, Najeriya ta ci gaba da sa ido kan sauran mutane 52 da aka gano sun yi mu’amala da ita. Hukumomin lafiya sun jaddada muhimmancin ci gaba da bibiyar waɗanda suka yi mu’amala da majinyaciyar, domin gano duk wata alama da zata iya nuna kamuwa da cutar da wuri.
Gwamnatin tarayya da NCDC sun ƙarfafa matakan da ake ɗauka domin hana yaɗuwar cutar zuwa wasu mutane.
Waɗannan matakai sun haɗa da gano mutanen da suka yi mu’amala da majinyaciyar, sa ido kan lafiyarsu, gudanar da gwaje-gwaje idan an ga buƙata, da kuma tabbatar da cewa ma’aikatan lafiya suna bin ƙa’idojin kariya yayin kula da marasa lafiya.
A ranar 23 ga Oktoba, an kuma samun rahoton wani wanda ake zargin ya kamu da cutar a Jihar Rivers. Sai dai sakamakon gwaje-gwajen dakin gwaje-gwaje ya nuna cewa bai kamu da cutar Ebola ba.
Hakan ya nuna muhimmancin yin gwaje-gwaje domin tabbatar da ko mutum ya kamu da cutar, maimakon dogaro da alamomin rashin lafiya kaɗai.
Hukumar NCDC ta bukaci ’yan Najeriya su kasance masu lura da lafiyarsu, su kuma bi sahihan bayanai da hukumomin lafiya ke fitarwa.
Duk da cewa an dauke majinyaciyar zuwa Switzerland domin ci gaba da jinya, hukumomin lafiya sun bayyana cewa aikin dakile cutar a Najeriya bai tsaya ba. Dole a cigaba da lura da kuma yin gwaje-gwajen da ya kamata.
Hukumomin lafiya sun jaddada cewa samun sauƙin majinyaciyar abin ƙarfafa gwiwa ne, amma ba ya nufin an kawo ƙarshen haɗarin cutar. Saboda haka, ci gaba da bin ƙa’idojin kariya da sa ido kan waɗanda suka yi mu’amala da ita na da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a. Sun shawarci al’umma da su kasance cikin natsuwa, tare da guje wa yada jita-jita ko bayanan da ba su fito daga sahihan majiyoyi ba game da barkewar cutar Ebola.
Sun kuma jaddada muhimmancin kai rahoton duk wani alamun rashin lafiya da ake zargin yana da alaƙa da cutar ga cibiyoyin lafiya, domin samun bincike da kulawa cikin gaggawa.
Masana lafiya sun bayyana cewa gano cutar da wuri, bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da majinyata da kuma bin ƙa’idojin kariya na daga cikin muhimman hanyoyin dakile yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa.
Ana shawartar mutane da su guji yaɗa sunaye, hotuna ko bayanan sirri na majinyata ba tare da izini ba. Kare sirrin waɗanda suka kamu da cuta yana da muhimmanci wajen mutunta haƙƙinsu, tare da tabbatar da cewa ba a mayar da yanayin lafiyarsu sanadin cin zarafi ko nuna musu wariya ba.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







