Labarai Morganable Hausa

Ƙasashe 120 Sun Zuba Jari A Matatar Dangote

Ƙasashe 120 Sun Zuba Jari A Matatar Dangote. Kimanin ƙasashe 120 ne suka sayi hannun jarin Matatar Mai ta Dangote.

Ƙasashe 120 Sun Zuba Jari a Matatar Dangote
Hoton Dangote
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Kimanin ƙasashe 120 ne suka sayi hannun jarin Matatar Mai ta Dangote, inda adadin buƙatar hannun jarin ya kai har ninki uku na abin da kamfanin ya tanada domin sayarwa.

Kamfanin Dangote ne ya bayyana hakan bayan kammala cinikin hannun jarin a ranar Talata, bayan ya ƙara wa’adin sayarwar da makonni biyu. Kamfanin ya ce ya samu gagarumar nasara a shirin sayar da kashi 30 cikin 100 na hannun jarin matatar, wanda aka kimanta kan dala biliyan 1.6.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan cinikin sun bayyana cewa buƙatar hannun jarin ta ninka har sau uku na adadin da aka tanada.

Rahoton ya kuma bayyana cewa masu zuba jari daga Najeriya sun yi alƙawarin saka naira tiriliyan 6.4, kwatankwacin dala biliyan 4.78.

Kamfanin Dangote ya bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga nahiyar Afirka, yana mai cewa haɗin kan al’ummar Afirka zai taimaka musu wajen cimma manyan manufofi.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce masu zuba jarin sun fito ne daga dukkan ƙasashen Afirka 54, se waɗanda suka fito daga sauran sassan duniya.

An gina matatar ne kan kuɗi dala biliyan 20, kuma tana da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 700,000 a kowace rana.

Kamfanin ya ce yana da shirin faɗaɗa matatar domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kullum. Idan aka kammala wannan shiri, matatar za ta zarce matatar Jamnagar da ke ƙasar Indiya wajen girma.

A watan Yulin da ya gabata, matatar ta sayar da hannun jari na dala biliyan 2.5 ga wasu zaɓaɓɓun masu zuba jari, kafin daga bisani ta buɗe damar sayen hannun jarin ga sauran jama’a.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa za a fara bai wa masu zuba jarin hannun jarin da suka saya daga mako mai zuwa, kafin a shigar da shi kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

Tun bayan fara aiki a shekarar 2023, matatar ta taimaka wajen samar da man fetur da sauran kayayyakin mai a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.

A lokacin rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, an bayyana cewa matatar ta taimaka wajen samar da iskar gas da man jiragen sama ga Amurka da wasu ƙasashen Turai, a lokacin da farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya.

Bayan buɗe damar sayen hannun jarin Matatar Dangote, harkar kasuwancin hannayen jari ta ƙara jan hankalin jama’a da dama. Wannan ne ya sa aka yi ƙarin bayani kan ma’anar hannun jari, yadda ake saye da sayarwa da kuma matakan da mutum ya kamata ya bi kafin ya saka kuɗinsa.

A wani bincike da aka gudanar kan wannan batu, an tattauna da Dakta Abdussalam Kani, malami a Sashen Tattalin Arziki na Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Jihar Kano, domin ya yi bayani dalla-dalla kan yadda harkar take.

A cewarsa, hannun jari na nufin kuɗin da mutum ya saka a wani kamfani ko kasuwanci domin ya mallaki kaso a cikinsa. Kamfanin zai yi amfani da kuɗin wajen gudanar da ayyukansa, sannan idan aka samu riba, mai hannun jarin zai iya samun nasa kaso bisa adadin jarin da ya mallaka da kuma tsarin rabon ribar kamfanin.

Ya bayyana cewa idan mutum ya saka naira dubu ɗaya, ba za a ba shi rabon riba daidai da wanda ya saka naira dubu biyu ko dubu goma ba, domin ana la’akari da adadin jarin da kowa ya zuba.

A cewarsa, hannun jari ya kasu gida biyu: hannun jari na masu kamfani kaɗai (Private Shares) da kuma hannun jari da aka buɗe wa jama’a (Public Shares).

Ya ce hannun jari na masu kamfani kaɗai yana kasancewa ne ga waɗanda suka kafa kamfanin ko kuma waɗanda aka ba su damar mallakar kaso a cikinsa.

Sai dai hannun jarin da aka buɗe wa jama’a yana ba duk wanda yake da sha’awar zuba jari damar saye, ko da kuwa ba ya cikin waɗanda suka kafa kamfanin ba.

Dakta Kani ya bayyana cewa sayar da hannun jari na taimaka wa kamfanoni wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu ba tare da sun dogara kacokan da karɓar bashi daga bankuna ba.

Ya ce idan kamfani ya nemi bashi daga banki, hakan na iya ɗaukar lokaci, sannan a gindaya masa wasu sharudda tare da cajin kuɗin ruwa. Amma ta hanyar sayar da hannun jari, kamfani na iya tara kuɗin da yake buƙata daga masu zuba jari.

A bangaren jama’a kuma, ya ce hannun jari na ba wa mutanen da ke da ɗan tanadin kuɗi damar saka su a kamfani domin samun damar cin gajiyar ribar da za a samu.

Ya bayyana cewa wannan na iya taimaka wa ma’aikata ko wasu mutane da ba sa gudanar da kasuwanci kai tsaye wajen samun ƙarin kuɗin shiga, wanda zai iya taimaka musu wajen biyan buƙatun rayuwa kamar kuɗin haya da na makaranta.

Ya ƙara da cewa zuba jari na taimaka wa tattalin arziki ta hanyar samar da kuɗaɗen faɗaɗa kamfanoni, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Da yake magana kan matatar Dangote, Dakta Kani ya ce sayar da hannun jarin zai taimaka wa kamfanin wajen tara kuɗin da yake buƙata domin faɗaɗa ayyukansa da ƙara ƙarfin tace mai.

Ya bayyana cewa idan kamfanin ya samu kuɗaɗen da yake nema, hakan zai iya ba shi damar faɗaɗa ayyukansa, samar da ƙarin guraben aikin yi da kuma taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya kuma ce wannan dama ce ga jama’a su mallaki kaso a matatar, ta yadda za su iya cin gajiyar rabon ribar da kamfanin zai iya bayarwa idan ya samu riba.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights