Labarai Morganable Hausa

Yan Bindiga Sun Sace Jariri Dan Wata Daya A Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace Jariri Dan Wata Daya A Kaduna

An yi zargin sace mutum biyar, ciki har da jariri mai kimanin wata guda.

Yan Bindiga Sun Sace Jariri Dan Wata Daya A Kaduna
Hoton daji
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

An yi zargin sace mutum biyar, ciki har da jariri mai kimanin wata guda, a Mararaban Kajuru da ke ƙaramar hukumar Kajuru.

Rahoton tsaro na al’umma ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026 Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Kaduna da ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar ba su fitar da sanarwar jama’a kan lamarin ba.

Jaridar Legit Hausa ta bayyana cewa; wani saƙon bayanin halin tsaro da ake yaɗawa a cikin al’umma ya bayyana cewa an sace mutanen ne a yankin da daren ranar Talata. Saƙon ya ce: 

“Wannan saƙo ne domin sanar da mu halin tsaro a Mararaban Kajuru da sanyin safiyar yau, Talata, 20 ga watan Oktoban 2026.” “Da misalin ƙarfe 1:00 na dare, a Mararaban Kajuru da ke gundumar Kufana, ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, an tabbatar da sace mutum biyar, ciki har da jariri mai wata guda, a safiyar yau.” 

Wannan lamari ya sake jawo hankalin Jama’a kan matsalar tsaro da kuma barazanar da garkuwa da mutane ke cigaba da haifarwa ga mazauna wasu yankunan a Arewacin Nigeria.

Lamarin ya tayar da hankalin Jama’a saboda jaririn da aka sace wanda ko wata biyu be cika ba, da kuma hadarin da zai iya fuskanta idan ya dade babu kulawa mai kyau.

Wadannan hare-hare na nuna yadda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da gudanar da danyen aiki ba tare da tausayawa jarirai ko mata masu juna biyu ba. Gwamnati da jami’an tsaro na ci gaba da fadi-tashin ganin an shawo kan wannan matsala ta rashin tsaro a jihar.

Bayanan da aka samu bai yi cikaken bayani kan yadda maharan suka isa yankin ba, ko gidan da suka shiga da yadda akai har suka tawo da jariri dan wata daya ba. An de sanar da an sace mutum biyar a ranar Talata ciki harda jariri dan wata daya.

Sannan kuma, ba’a bayyana ko an samu raunuka ko asarar rayuka yayin da lamarin ya faru ko kuma wani abu game da mahaifiyar jaririn ba. Babu sunayen mutanen da akayi garkuwa da su, kuma sannan babu cikakken bayani akan iyalansu ko halin da suke ciki. Sannan babu wanda ya fito yace yana daga cikin yen uwan wayenda aka sace.

Bayanan tsaro da aka yada yayi kira ga al’umma da suyi addu’ar dawo da mutanen da aka yi garkuwa dasu cikin koshin lafiya. Sannan kuma su guji yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Wannan na nuna damuwar da mutane ke ciki a duk lokacin da aka samu rahotan sace mutane, musamman idan harin ya shafi yara kanana, mata da sauran mutanen da basu da ikon kare kansu ko biyan kudin fansa.

Rundunar yan sandan jihar Kaduna da Ma’aikatar Tsaron cikin Gida ta jihar basu fitar da sanarwa ba da kuma cikakken bayani kan lamarin sace mutanen ba. Wannan na nufin cewa, duk da kafafen yada labarai sun yada lamarin, akwai bukatar samun karin bayani daga hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cikakkun bayanai.

Hukumomin tsaro su ne za su iya bayyana cewa ko sun samu rahoton sace mutanen, ko an fara bincike, ko an nemi kudin fansa ko kuma an dauki matakan da za’a kubutar da su.

Garkuwa da mutane na daya daga cikin matsalolin tsaro da ke jefa iyalai cikin fargaba da tsoro. Idan aka yi garkuwa da mutum, yan uwa na shiga cikin yanayi na damuwa, fargaba, tsoro, tunanin yadda za’ayi su fanshi ran dan uwansu. Saboda  ba su san inda yake ba, halin da yake ciki, ze dawo a raye ko kuma akasin haka.

Wannan lamarin ya sa hankalin mutane ya tashi sosai bayan la’akari da jariri dan wata daya cikin wadanda aka sace. Duk da cewa babu isasshen bayanin da zai tabbatar da halin da jaririn yake ciki a yanzu ba. Jarirai na bukatar uwa a tare da su wajen ba su abinci, kulawa akai-akai, muhali mai kyau, tsaftar waje da na tufafi tare da kariya daga yanayin da zai iya cutar da lafiyarsu.

Al’umma na bukatar hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a Jihar Kaduna da su taimaka wajen bayyana wa mutane halin da ake ciki. Tare da sanar da duk wani muhimman bayanai da aka samu.

Idan an tabbatar da an sace mutanen, yana da mahimmanci a gudanar da bincike tare da daukar matakan da suka dace domin gano inda suke. Jama’a ma zasu iya taimakawa hukuma wajen bayarda sahihan bayanai da zasu taimaka wajen bincike, ba yada jita-jita ba.

Masu amfani da kafafen sada zumunta suma suna da rawar da zasu taka wajen bada tasu gudunmawar dan kwato wayenda aka sace.

A takaice, rahotannin Legit.ng Hausa da Leadership Hausa sun bayyana cewa a Mararaban Kajuru da sanyin safiyar Talata, 20 ga watan Oktoban 2026. Da misalin ƙarfe 1:00 na dare, a Mararaban Kajuru da ke gundumar Kufana, ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, an tabbatar da sace mutum biyar, ciki har da jariri mai wata guda.

Sai dai har zuwa yanzu ba’a bayyana sunayen mutanen ba, kuma hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwa ba dangane da lamarin ko kuma bayani kan ko an kubutar da mutanen ko kuma anji wani labari da zai sa a san halin da suke ciki. Amma duk da haka mutane na sa ran samun wani bayani daga jami’an tsaro dan sanin halin da wayenda aka sace suke ciki.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights