Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak
Kotu Ta Ba Da Belin Yar Jarida Farida Isiak
An bayar da belin Farida Isiak, wata yar yarda mai shekaru 23 da aka tsare tare da iyayenta

Mahangar Labari
KANO —
An bayar da belin Farida Isiak, wata ‘yar jarida mai shekaru 23 da aka tsare tare da iyayenta bayan rikici kan sayar da gawayi da ya faru tsakanin mahaifiyar matashiyar da makwabciyarta, a jihar Kaduna bayan kotu ta soke hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da aka yanke mata.
Lauyanta, Mukhtar Abubakar, ne ya ƙalubalanci shari’ar, yana mai cewa an yanke mata hukunci ne bayan ta amsa laifi ba tare da wakilcin lauyanta ba, kuma ba ta fahimci illar amsa laifin da ta yi ba. Dan haka ya nemi da a bada belin ta bayan yadda yaga an yanke mata hukinci da gaggawa.
Wata kotu da ke zamanta a Kawo, a ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa da ke jihar Kaduna, ta bayar da belin matashiyar ’yar jarida, Farida Isiak, mai shekaru 23, wadda jami’an ’yan sanda suka tsare tare da iyayenta a Mararaban Jos, sakamakon wani saɓani da ya shiga tsakanin mahaifiyarta da wata maƙwabciyarsu kan sayen gawayi.
Alƙalin kotun, Alhaji Tureta, ya bayar da belin Farida har zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Rikicin ya samo asali ne bayan sun sami saɓani da ya shafi sayen gawayi. Sai dai, ana zargin cewa akwai rashin jituwa tsakanin ’yan sanda da ma’aikatan gidan rediyon Nagarta.
An rawaito cewa Farida, wadda ke aiki a gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna, an kai ta ofishin ’yan sanda da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar 20 ga watan Oktoba, bayan an riga an tsare iyayenta.
Wani ɗan gidan ya bayyana cewa Farida ta samu labarin kama mahaifiyarta ne a lokacin da take wurin aiki. Bayan samun labarin, ta wallafa saƙo a shafinta na Facebook, inda ta soki ’yan sanda kan lamarin. Da kuma yadda basu yi mata adalci ba wanda ya kai ga har sun kama iyayenta ba tare da sunyi bincike a kan lamarin ba.
Sede shugaban gidan rediyon Nagarta, Alhaji Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya bayyana cewa gidan rediyon ba shi da hannu a rikicin da ya faru tsakanin iyalan Farida da maƙwabtansu.
Sai dai, ya yi nuni da cewa an daɗe ana samun rashin jituwa tsakanin wasu jami’an ’yan sanda da ma’aikatan gidan rediyon, sakamakon yadda kafar yaɗa labaran ta rawaito batun kisan wata malama a garin Mararaban Jos da akayi a kwanakin baya a garin.
Yero ya buƙaci ’yan jarida da su guji wallafa duk wani abu a shafukan sada zumunta da kan iya janyo musu matsala, tare da yin taka-tsantsan don kauce wa shiga irin waɗannan rigingimu.
A cikin wata sanarwar da ƙungiyar Amnesty International tayi, ta buƙaci a janye tuhumar da ake yi wa ’yar jaridar, Farida Isiak, wadda jami’in ’yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka (DPO) na Mararaban Jos, Usman Adamu, ya gurfanar a gaban kotun majistare. Rahoton ya ce kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari ko biyan tarar naira miliyan 1.7.
Amnesty ta bayyana cewa abin da ya jawo wa Farida matsala shi ne sukar da ta yi wa ’yan sanda dangane da yadda suka tsare mahaifiyarta, bayan wani rikici da ya shiga tsakaninta da maƙwabciyarta kan cinikin gawayi na naira 100 a shafinta na Facebook.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda sun kama mahaifiyar Farida ne sakamakon rikicin, sannan suka tsare mahaifinta bayan ya je neman belinta. Daga bisani, sun nemi Farida ta bayyana a gabansu saboda sukar da ta yi musu a shafinta na Facebook.
A cewar Amnesty, lokacin da Farida ta je ofishin ’yan sanda, sai suka tsare ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun majistare da ke Kawo. Kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu, a cikin shari’ar da aka kammala cikin ƙasa da sa’o’i 24.
Ƙungiyar ta ce yadda aka kama Farida, aka gurfanar da ita a gaban kotu, sannan aka yanke mata hukunci, ya saɓa wa ƙa’idojin shari’a. Saboda haka, ta buƙaci kwamishinan ’yan sandan jihar Kaduna da hukumomin shari’a na jihar su gaggauta duba lamarin domin tabbatar da an yi wa Farida adalci.
Jaridar Premium Times ta bayyana mana cewa Lauyan Farida Abubakar ya ce ya isa kotun ne lokacin da ake shirin kai Farida gidan gyaran hali bayan an yanke mata hukunci.
Ya bayyana cewa an gurfanar da ita, ta amsa laifi, sannan aka yanke mata hukunci kafin lauyoyinta su iso.
Ya ce tawagar lauyoyin ta shiga tsakani, inda suka bayyana cewa Farida ba ta fahimci yadda shari’ar ta gudana da kuma sakamakon amsa laifin da ta yi ba.
Lauyan ya ƙara da cewa an sanar da kotun cewa lauyoyinta na kan hanyarsu ta zuwa, amma aka ci gaba da shari’ar ba tare da su ba.
Bayan mai gabatar da ƙara ya amince cewa akwai dalilan sake duba shari’ar, kotun ta soke shari’ar farko da hukuncin da aka yanke wa Farida, sannan ta ba ta damar sake amsa tuhume-tuhumen.
Farida ta tabbatar wa PREMIUM TIMES bayan sakinta cewa ita ce ta wallafa saƙon a Facebook ɗin da aka goge.
Haka kuma, Amnesty ta yi kira ga rundunar ’yan sandan Najeriya da ta gudanar da bincike kan rawar da jami’anta suka taka wajen tsare Farida da kuma gurfanar da ita a gaban kotu cikin gaggawa, ba tare da gudanar da cikakken bincike ba.
A cewar Amnesty, lokacin da Farida ta je ofishin ’yan sanda, sai suka tsare ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun majistare da ke Kawo. Kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu, a cikin shari’ar da aka kammala cikin ƙasa da sa’o’i 24 Wanda ba haka ya dace a gudanar da shari’ar ba.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







