Babu Maganin Nau’in Ebolar Da Ta Ɓulla A Nijeriya – WHO
Babu Maganin Nau’in Ebolar Da Ta Ɓulla A Nijeriya – WHO. WHO Ta Tabbatar da Nau’in Ebola da Aka Gano a Abuja

Mahangar Labari
KANO —
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa nau’in cutar Ebola da aka gano a Abuja shi ne Bundibugyo, yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da ɗaukar matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar. Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu babu takamaiman magani ko allurar rigakafi da aka amince da su domin yaƙi da wannan nau’in cutar.
Bayanai sun nuna cewa majinyaciyar da aka gano tana ɗauke da cutar ta shigo Nijeriya daga ƙasar Uganda a ranar 3 ga Oktoba, ta jirgin saman Ethiopian Airlines. Wannan lamari ya jawo hankalin hukumomin lafiya, inda aka fara gudanar da bincike domin gano mutanen da suka yi hulɗa da ita da kuma waɗanda ka iya kasancewa cikin haɗarin kamuwa da cutar.
A halin yanzu, hukumomin lafiya sun gano mutane 44 da suka yi hulɗa da majinyaciyar, yayin da ake ci gaba da neman ƙarin mutanen da zasu iya kasancewa cikin haɗarin kamuwa da cutar. Ana gudanar da wannan bincike ne domin gano duk waɗanda suka yi mu’amala da ita, ta yadda za a iya ɗaukar matakan da suka dace domin kare lafiyarsu da ta sauran jama’a.
Neman waɗanda suka yi hulɗa da majinyaciyar na daga cikin muhimman matakan da ake ɗauka a irin wannan yanayi domin hana yaduwar cutar.
Hakan na taimakawa wajen gano mutanen da za su buƙaci kulawa ko sa ido, tare da rage yiwuwar cutar ta bazu zuwa wasu mutane ba tare da an gano hakan da wuri ba.
A wani mataki da aka dauka wajen samun cikakken bayani kan lamarin cutar, gwamnatin Uganda ta nemi gwamnatin Nijeriya da ta ba ta cikakkun bayanai game da tafiye-tafiyen matar da kuma tarihin jinyarta. Wannan buƙata ta zo ne yayin da ake ƙoƙarin gano yadda lamarin ya faru da kuma wuraren da ya kamata hukumomin lafiya su mayar da hankali a kansu.
Gwamnatin Uganda ta bayyana cewa kasancewar matar ta bi ta ƙasar a yayin tafiyarta ba yana tabbatar da cewa a can ta kamu da cutar ba. Saboda haka, akwai buƙatar gudanar da cikakken bincike kan tarihin tafiyarta da sauran bayanan da suka shafi lafiyarta kafin a iya cimma matsaya kan inda ta kamu da cutar.
Wannan batu na nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe wajen binciken cututtukan da za su iya yaɗuwa daga wannan wuri zuwa wani don kare lafiyar al’umma. Idan majinyaci ya yi tafiya tsakanin ƙasashe, bayanan da suka shafi tafiyarsa da mutanen da ya haɗu da su na iya taimakawa wajen gano yiwuwar hanyoyin yaɗuwar cutar da kuma ɗaukar matakan kariya.
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana aiki tare da gwamnatin Uganda domin shawo kan lamarin da kuma ɗaukar matakan da suka dace don hana yaɗuwar cutar. Wannan haɗin gwiwa na da muhimmanci wajen daidaita matakan da hukumomin lafiya na ƙasashen biyu za su ɗauka.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba. Ta jaddada muhimmancin dogaro da bayanan da hukumomi, likitoci da bangaren da abin ya shafa suka tabbatar, maimakon yaɗa jita-jita da za su iya haifar da fargaba ko ruɗani a tsakanin al’umma.
Masana harkokin lafiya suna kara jan hankalin mutane kan samar da muhimman bayanai a lokacin da ake fuskantar barazanar wata cuta mai yaɗuwa. Idan aka yaɗa bayanan da ba su da tushe, hakan na iya sa jama’a su ɗauki matakan da ba su dace ba ko kuma su yi watsi da shawarwarin kariya da hukumomin lafiya suka bayar.
Saboda haka, ana buƙatar jama’a su riƙa sauraron sanarwar hukuma tare da bin shawarwarin da aka bayar domin kare kansu da sauran mutane.
Sannan ya kamata a guji ɗaukar duk wani rahoto da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a matsayin gaskiya, musamman idan ba a san tushensa ba.
A wani mataki na ƙarfafa kariya daga cututtuka masu yaɗuwa, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun buƙaci a riƙa gudanar da binciken lafiyar dukkanin matafiya a filayen jiragen sama da tashoshin sufuri.
Wannan mataki na nufin taimakawa wajen gano mutanen da suke ɗauke da cututtuka tun da wuri, domin hakan ze bada nasara wajen iya ɗaukar matakan da suka dace kafin matsalar ta ƙara karuwa.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun bayyana cewa kiran ‘yan majalisar nada muhimmancin domin hakan ze sa a sanya ido kan lafiyar matafiya, musamman waɗanda ke shigowa ƙasar daga ƙasashen waje.
Binciken lafiya a wuraren shiga da fita na iya taimakawa wajen gano alamomin da ke buƙatar ƙarin kulawar likitoci, ko kuma gano mutanen da ya kamata a duba su domin kare sauran al’umma ko kuma shigo da wani sabon abu da ze iya cutar da mutane.
Sai dai, ana buƙatar irin waɗannan matakai su kasance cikin tsari tare da bin ƙa’idojin lafiya, domin tabbatar da cewa ana kare jama’a ba tare da haifar da tsoro ko yaɗa bayanan da ba su tabbata ba.
Haka kuma, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin lafiya, ma’aikatan sufuri, gwamnati da sauran hukumomin da ke kula da matafiya na iya taimakawa wajen aiwatar da matakan kariya yadda ya kamata.
Duk da cewa hukumomi sun fara ɗaukar matakai kan lamarin, har yanzu ana buƙatar ci gaba da bincike domin samun cikakken bayani game da tafiyar majinyaciyar, mutanen da ta yi hulɗa da su da kuma yiwuwar haɗarin da ke tattare da lamarin dan kar abin ya shafi wasu bangarori.
A ƙarshe, ana sa ran haɗin gwiwar Nijeriya da Uganda, tare da matakan da hukumomin lafiya ke ɗauka cewar za su taimaka wajen gano waɗanda za su iya kasancewa cikin haɗari da kuma rage yiwuwar yaɗuwar cutar. A halin yanzu, ana kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita, tare da bin shawarwarin hukumomin lafiya yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.
Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.







