Labarai Morganable Hausa

INEC Ta Warware Ƙorafe-Ƙorafen Wasu ’Yan Takarar 2027

INEC Ta Warware Ƙorafe-Ƙorafen Wasu ’Yan Takarar 2027. Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) ta kammala duba ƙorafe-ƙorafen da aka shigar mata.

INEC Ta Warware Ƙorafe-Ƙorafen Wasu ’Yan Takarar 202
Hoton Rajistar Zabe Wato INEC
HANYAR KARATU

Mahangar Labari

Sashe Labarai
Nau’in Labari Rahoto
Asalin Labari Asali a Hausa
Lokacin Karatu 5 min
Wuri Kano

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar a ranar Alhamis cewa ta kammala duba ƙorafe-ƙorafen da wasu jam’iyyu da ’yan takarar gwamna suka shigar mata, inda ta ce an samu damar dawo da wasu sunayen ’yan takarar da aka cire a baya domin su ci gaba da takara a zaɓen 2027.

Sai dai har yanzu hukumar ba ta wallafa sabon jerin sunayen ’yan takarar da ta tantance ba. Haka kuma, wasu daga cikin ’yan takarar sun shaida wa BBC cewa INEC ba ta tuntube su a hukumance domin sanar da su sakamakon ƙorafe-ƙorafen nasu ba.

A ranar 10 ga Oktoban da muke ciki ne INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohin ƙasar. Bayan wallafa jerin sunayen, wasu jam’iyyu sun nuna rashin gamsuwarsu, inda suka ce ba su ga sunayen ’yan takararsu na wasu muƙamai ba.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe sama da 60 tun bayan wallafa jerin sunayen ’yan takarar gwamna.

A sanarwar da shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar, INEC ta ce ta nazarci ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyun suka shigar, tare da la’akari da hukuncin da kotuna suka yanke kan wasu batutuwa.

Ta ce bayan wannan nazari, ta samu dalilan da suka dace na mayar da wasu sunayen cikin jerin ’yan takarar.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da ba ta samu isassun hujjojin da za su tabbatar da su ba.

INEC ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyu 12 a jihohi 26 dangane da takarar gwamna. Daga cikin waɗannan ƙorafe-ƙorafe, ta ce ta warware guda 41, yayin da ta yi watsi da 26.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta cire wasu sunaye da aka saka a jerin farko bayan gano cewa an yi kuskure wajen shigar da su.

Ta ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za ta aika da sunayen jam’iyyu da ’yan takarar da batun ya shafa zuwa ofisoshinta na jihohin da abin ya shafa.

A cikin sanarwar, INEC ba ta ambaci sunayen mutanen da ta mayar cikin jerin ’yan takarar ba. Haka kuma, ba ta bayyana waɗanda aka tabbatar da cire sunayensu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen ba.

Abin da hukumar ta bayyana kawai shi ne ta warware ƙorafe-ƙorafe 41, tare da yin watsi da guda 26.

Ta kuma ce za ta aika da cikakkun sunayen jam’iyyu da ’yan takarar da batun ya shafa zuwa ofisoshinta na jihohin da abin ya shafa nan ba da jimawa ba.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar domin jin sunayen ’yan takarar da suka samu nasarar komawa cikin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027, amma ba a samu cikakken bayani kan hakan ba.

Wasu daga cikin ɓangarorin da abin ya shafa sun shaida wa BBC cewa har yanzu INEC ba ta tuntube su a hukumance domin sanar da su matsayarta kan batun dawo da sunayen ’yan takararsu ba.

Kakakin jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya shaida wa BBC cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto a safiyar Juma’a, hukumar ba ta sanar da su matsayarta a hukumance ba.

Ya ce INEC ta sanar da su cewa sashen shari’a na hukumar zai fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar da ta amince da ƙorafe-ƙorafensu nan ba da jimawa ba.

Dukku ya ƙara da cewa bayan fitar sanarwar, ya tuntubi shugabancin jam’iyyar na ƙasa domin jin ko INEC ta aika musu da wata sanarwa a hukumance kan batun, amma har yanzu ba su samu irin wannan sanarwa ba.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ma bai samu wata sanarwa daga INEC da ke tabbatar da cewa an mayar da sunansa cikin jerin ’yan takarar ba.

Da yake magana da BBC, kakakin Kwankwasiyya na Najeriya, Habibu Sale Mailemo, ya ce suna jiran hukumar ta fitar da cikakken jerin sunayen, kuma suna fatan za su ga sunan ɗan takararsu a ciki.

Ya ce, a cewarsu, INEC ta nuna cewa ba ta da matsala da su ta fuskar cancanta ko kuma kasancewar sunan ɗan takararsu a rajistar ’yan jam’iyya.

Sai dai ya jaddada cewa har yanzu ba su samu wata takarda daga hukumar da ke tabbatar da dawo da sunan ɗan takararsu ba.

Ya ce sun fahimci cewa INEC ta sake nazarin ƙorafe-ƙorafen ne, ta bayyana matsayarta, sannan ta ce za ta fitar da sunayen a ofisoshinta.

Mailemo ya ƙara da cewa za su ci gaba da bibiyar sanarwar hukumar da shafukanta domin ganin lokacin da za ta wallafa cikakken jerin sunayen.

Wata majiya a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana cewa hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa kan cire sunayen wasu ’yan takara ko kuma rashin saka su cikin jerin masu neman kujerun gwamna da na majalisun dokokin jihohi.

Majiyar ta ce kusan ƙorafe-ƙorafe 36 ne suka yi nasara, yayin da sauran ba su samu nasara ba.

“Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa. Wasu sun yi nasara, ina ganin kusan 36, yayin da sauran ba su yi nasara ba,” in ji majiyar.

Sai dai ta ƙara da cewa hukumar na jiran sashen shari’arta ya tabbatar da cikakken adadin ƙorafe-ƙorafen da aka amince da su. A cewarta, sashen ne ke shirya sanarwar da za a fitar domin bayyana hukuncin da aka yanke kan ƙorafe-ƙorafen.

MORGANABLE HAUSA · BRIEFING

Kada mu tsaya a wannan labarin kawai.

Yi rajista domin samun zaɓaɓɓun rahotanni, nazari da muhimman abubuwan da Morganable Hausa ke bibiyarsu.

LABARAI · NAZARI · ABIN DA ZA A SA IDO Yi rajista

Barka da dawowa!

Shiga asusunka a ƙasa.

Maido da kalmar sirrinka

Please enter your username or email address to reset your password.

Ƙara sabon jerin bidiyo

Verified by MonsterInsights